Akalla fasinjoji 15 da suka hada da mata da yara ne suka bace a wani hari da mahara suka kai wa wata motar kirar bas mai dauke mutane 18 da ta taso daga Zaki/Biam a Jihar Benue zuwa Maihura a Karamar Hukumar Bali ta Jihar Taraba.
Maharan dauke da muggan makamai sun kai wa motar hari a kauyen Gamkwe da ke Maraban-Baisa a Karamar Hukumar Donga a jihar.
- Barcelona Ta Kai Matakin Kwata Final A Gasar Zakarun Turai Bayan Shekara 4
- Tinubu Ya Bai Wa Gwamnoni Mako 2 Su Kawo Karshen Matsalar Manoma Da Makiyaya
Direban bas din, Mista Mpuuga Mbaave wanda ya tsallake rijiya da baya, ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce yana zargin ‘yan banga ne suka kai harin.
“Na yi lodin fasinjoji 18 daga Zaki/Biam, kawai sai na hangi mutane da yawa, na yi zargin cewa wani abu ne ya faru, sai na tsaya amma daya daga cikin fasinjojin ya ce min na tafi amma na ki.
“Da na matsa kusa, sai wasu daga cikin ‘yan bangar suka fara ihu, suna cewa kashe su, su ne suka kashe mambobinmu, sai suka fara saran fasinjojinmu da adduna.
“Sun kwashe mu gaba daya, suka tilasta mana muka kwanta, motata tana kunne da na ga lamarin na neman kacamewa sai fice na bar fasinjojin, shi ma yaron motata ya biyo ni, kuma duk sun sare mu da adda ga jini ko ina a jikinmu, ta haka muka tsira muka bar fasinjojin a can,” in ji Mpuuga.
Shugaban Karamar Hukumar Doonga, Hon. Ezra Voka ya tabbatar wa LEADERSHIP faruwar lamarin ta wayar tarho, inda ya ce tuni ya je dajin da ke kusa da wajen don neman fasinjojin.
“Abokina, ina daji don neman mutanen da suka bace, ba zan iya magana ta yawa ba har sai lokacin da na samu karin bayani daga nan,” in ji Voka.