Hukumar raya babban birnin tarayya FCTA ta rusa sansanin ‘yan fashi da kasuwannin da ba a saba gani ba a unguwar Lugbe dake kan titin filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke yankin.
Babban mataimaki na musamman kan sa ido, dubawa da aiwatarwa ga ministar babban birnin tarayya Abuja, Ikharo Attah, wanda ya jagoranci tawagar rushe wuraren, ya bayyana cewa ayyukan barna da kasuwannin da ba a saba gani ba suna haifar da barna.
Ya ce mahadar rukunin gidaje na daya dana biyu na gidajen gwamnatin tarayya a yankin Lugbe yana da matukar muhimmanci da ake da bukatar su cika ka’idojin da suka dace, don haka ba za a bari a ci gaba da ayyukan da ba su dace ba a yankunan.
Attah ya ce ministan babban birnin tarayya, Malam Muhammad Bello, bayan ya duba yankin tare da tawagar jami’an tsaro a karshen mako.
Ya ci gaba da cewa, “Mun yi aikin share fage a kan titin filin jirgin a wasu lokutan da suka wuce amma ba zato ba tsammani sai a hankali ayyukan barna ke sake dawowa.
Ministan babban birnin tarayya Abuja ya ziyarci yankin Lugbe a karshen mako kuma ya ba da umarnin a dauki kwararan matakai.
“Kwamishanan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Sunday Babaji wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da aikin, ya ce dole ne a duba duk wasu haramtattun ayyuka da ke share fagen aikata laifuka a kan hanya.”
Attah ya bayyana cewa yawancin gidajen da aka rusa ba bisa ka’ida ba ana zargin maboyar masu laifi ne, inda ‘yan iskan ke shan tabar wiwi tare da amfani da wasu haramtattun kwayoyi cikin ‘yanci.
“Wasu jama’a da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda suka yi ta kokawa kan wadannan abubuwa marasa kyau a kusa da Lugbe a kan titin filin jirgin sama, yanzu za su iya kwana da idanuwansu biyu a rufe,” inji shi.
Wata ‘yar kasuwa da rugujewar ya shafa ba bisa ka’ida ba, Misis Rukiyat Abiodun, ta koka kan yadda jami’an babban birnin tarayya Abuja, ta ce kamata ya yi gwamnati ta yi la’akari da halin da ‘yan kasuwar ke ciki, ruguza shagunan nasu ba abu ne mai kyau ba.