Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, Gianni Infantino ya yi barazanar kin nuna gasar kofin duniya ta mata ga wasu kasashen Turai biyar, matakin da ya kawo cece-kuce a duniya.
Infantino ya bukaci kasashen da cewar sai idan kamfanonin da za su haska gasar a talabijin sun kara kudin tayin da suka yi tun farko kuma shugaban ya ce abin da takaici kan kudin da aka yi tayin tallata wasannin a Burtaniya da Sifaniya da Italiya da Jamus da kuma Faransa.
Ya kara da cewar an watsa wa ‘yan wasa da kwallon kafar mata kasa a ido, kuma manyan kasashen turai na shirin kawo koma baya a gasar wanda hakan abin takaici ne babba.
Za’a buga gasar kofin duniya ta mata a Australia da New Zealand da za’a fara ranar 20 ga watan Yulin wannan shekarar ta 2023 sai dai Infantino ya ce kamfanonin Turai da za su tallata gasar sun yi tayin biyan dalar Amurka miliyan daya zuwa miliyan 10 idan ka kwatanta da Dalar Amurka miliyan 100 zuwa miliyan 200 wajen tallata gasar kofin duniya ta maza.
Ya ce wannan tayin ba adalci, idan suka dage iya abin da za su biya kenan, hakan zai hana Fifa ta bayar da izinin nuna gasar a kasashen sannan ya kara da cewar dukkan kudin da za’a samu a kallon gasar ta bana za’a zuba su a fannin bunkasa kwallon kafar mata a duniya.
Infantino ya ce Fifa ta kara kudin ladan lashe kofin har linki uku zuwa Dalar Amurka miliyan 152, idan aka kwatanta da abin da ta biya gasar a 2019 a kasar Faransa da aka buga.
Haka kuma Fifa na fatan biyan ladan cin kofin duniya na mata ya zama bai daya da yadda ake bai wa maza daga nan zuwa 2026/27 kamar yadda aka amince a taron da ta gudanar a cikin watan Maris.
Kamar yadda Fifa ta sanar kimanin mutum biliyan 1.12 ne suka kalli gasar kofin duniya ta mata a Faransa a shekarar 2019 kuma ita ce gasar da mutane da yawa suka kalli kwallon kafar mata a tarihi.