Hukumar kwallon kafa ta FIFA za ta hukunta hukumar kwallon kafar Uruguay da ‘yan wasanta hudu kan halin rashin da’a a wasan da suka fafata da tawagar kasar Ghana a gasar cin kofin duniya.
Kasar Uruguay ce ta doke ta Ghana da ci 2-0 a wasan karshe na cikin rukuni na takwas a gasar cin kofin duniya ranar 2 ga watan Disamba kuma Uruguay ta karkare a mataki na uku a rukuni na takwas duk da cin Ghana da ta yi, inda Portugal da Koriya ta Kudu suka kai zagayen gaba.
‘Yan wasan Uruguay sun harzuka bayan tashi daga wasan, inda suka kalubalanci alkalin wasa da mataimakinsa kan zargi hana su bugun fenareti, bayan karo da aka yi tsakanin Alidu Seidu da Darwin Nunez.
Wadanda Fifa za ta hukunta daga Uruguay sun hada da Jose Maria Gimenez da Edinson Cabani da Fernando Muslera da kuma Diego Godin kuma kuma hukumar kwallon kafar Uruguay na fuskantar hukuncin rashin da’a da nuna banbanci.
Haka kuma FIFA na bincikar hukumar kwallon kafar Serbia a wasan da tawagarta ta buga da Switzerland a karawar karshe a rukuni na bakwai da suka tashi 3-2 sai dai FIFA ba ta fayyace laifin da Serbia ta aikata ba, amma an umarci magoya bayan tawagar da su daina rera wakar banbanci a lokacin wasannin su.