A yanzu dai za a iya cewa masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood likkafar ta ta kara ci gaba a fagen shirya fim inda a wannan lokacin ake ci gaba da daukar shirin fim na Turanci mai suna Princess Of Galma.
Shirin wanda kamfanin da ya saba shirya finafinan Turanci a Kannywood na Jammaje Productions kuma a ke aikinsa a cikin garin Kano a wannan lokacin, Galadima Muhammad ne ya ke bayar da umarni yayin da Jarumai irin su Magaji Mijinyawa. na Gidan Badamasi, Ishak Sidi Ishak, Hajara Makama, Faruk Sayyadi, Mustapha Musty, Zainab Bichi, Aisha A Musa, da sauran Jarumai da dama su ke cikin aikin.
Babban furodusan fim din Malam Kabiru Musa Jammaje, ya bayyana wa wakilinmu mnnufar fim din inda yake cewa.
“Shi wannan fim din Princess Of Galma mun yi shi ne kamar yadda muka saba shirya finafinai na Turanci a masana’antar Kannywood domin inganta fina-finanmu yadda zai yi daidai da yadda ake gudanar da finafinai a duniya, don haka ne ma a duk lokacin da muka tashi shirya finafinai a. kamfaninmu na Jammaje Productions muke kashe kudi sosai domin samar da fina-finai masu inaganci.”
Da yake bayani a kan labarin fim din kuwa, cewa ya yi.
“Asalin labarin dai na wata masarauta ne ta wani sarki da a ke kiran masarautar da sunan Galma, kuma ‘yarsa mace ce ita kadai, don haka sai a ke gudun kada ya mutu ya rasa magajii saboda mace ba ta yin mulkin masarautar don haka ake nema mata wanda za ta aura da zai zama sarkin idan mahaifinta ya rasu. Amma duk wanda ya zo neman aurenta ba ta sauraron sa. Sai ya zama a cikin mafarki ta hadu da wanda take son ta aure har aka yi soyayya aka yi auren duk a mafarki. Don haka mun zo da wani tsari ne da ya zama bako a cikin harkar fim din Kannywood wanda dama burinmu shi ne samar da sauyi ta kowanne bangare a cikin harkar yadda za ta samu ta ci gaba da bunkasa.”
Ya ci gaba da cewar “Duk da a yanzu an samu sauyi na yin fina-finai masu dogon zango. To mu za mu ci gaba da yin masu gajeren zango don nunawa a sinima da sauran dandamalin nuna fim na gidajen talbijin da ma ‘Internet’ Manufarmu dai samar da fim mai inganci a Kannywood wanda duniya za ta yi alfahari da shi, kuma muna sa ran zuwa karshen shekarar nan za a fara kallon fim din a Sinimu”.
Shi ma Magaji Mijinyawa, wanda ya fito a matsayin Sarki a cikin Princess Of Galma ya ce ” A gaskiya na ji dadin aikin wannan fim din, duk da na shafe tsawon shekaru ina fitowa a matsayin Jarumi a finafinan Turanci, to shi wannan da yake tsantsar al’adar Kassr Hausa a ke nunawa. abin ya burgeni sosai.kuma a shirye nake na bayar da duk wata gudummawa tawa don ganin an samu nasarar wannan aikin.”
Ita ma Jarumar Shirin da ta fito a matsayin Gimbiya Nafisa, wato Hajara Makama ta ce ” To ni sabuwa ce a Kannywood, amma dai na dan yi wasu fina-finai, sai dai babu wanda aka fi ba ni matsayi babba kamar wannan fim din Princess Of Galma da na fito a matsayin Jarumi, ina alfahari da shi kuma ina fatan fim din zai kara daga darajata a duniya.
Babban burina dai Princess Of Galma ya samu karbuwa sosai ta yadda nima darajata za ta kara girma.”
Galadima Muhammad, shi ne mai ba da umarni a fim din, ya shaida mana cewa ” Wannan aikin na Princess Of Galma na daban ne a cikin ayyukan da na saba yi na bayar da umarni, don haka na bayar da lokaci na baki daya don ganin an cimma nasarar da a ke so a samu a fim din, don haka ne ma ban dauki aikin da wasa ba. ina yin iya kokari na don na ga na yi abin da ya dace wajen gamsar da masu kallo.”
Zainab Bichi, wacce ta fito a matsayin kuyanga a fim din kuwa, cewa ta yi. ” Ka ga dai na saba fitowa a cikin finafinan Turanci har ma na Kudu, amma dai wannan tsarin fim din ya sha bamban da wamda na saba yi, kuma ina jin dadin aikin sosai don haka na ke yin a ikin cikin jin dadi.”
Babban burin da mutane dai su ke da shi ga wannan fim na Princess of Galma shi ne fatan kammala aikin cikin nasara, da kuma karbuwarsa a duninya, domin hakan ne zai kara daga martabar masana’antar fina-finai ta kannywood a duniya, saboda da ta yi fim da yaren Turancin da wasu su ke yi wa Kannywood kallon da ba za ta iya samar da fina-finai da harshen Turanci ba.