Fim na Nezha 2 na kasar Sin ya kara samun lambar yabo. A gun bikin nune-nunen littattafan zanen hotuna na kasa da kasa na kasar Sin karo na 18 da aka kaddamar a jiya 2 ga wannan wata, fina-finai guda 10 ciki har da fim na Nezha 2, da The Legend of Hei 2, da Curious Tales of a Temple sun samu lambobin yabo na Golden Dragon na kasar Sin karo na 22.
Ya zuwa yanzu, fim na Nezha 2 ya samu kudin tikitin kallo Yuan biliyan 15.44 a duniya gaba daya, yawan kudin tikitin fim din da aka samu a kasashen waje ya kai Yuan miliyan 400. Fim din ya hau matsayi na farko na fim na kagaggun hotuna da ya fi sayar da tikitin kallo a duniya, kana ya shiga jerin sunayen fina-finai na duniya guda 8 dake kan gaba wajen sayar da tikitin kallo. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp