Mataimakin mai horar da tawagar kwallon kafa ta Nijeriya ta Super Eagles kuma mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Enyimba da ke buga gasar Firimiya ta Nijeriya, Finidi George ne zai jagoranci tawagar Super Eagles a wasan sada zumunta da kasar Mali a mako mai zuwa.
Finidi shine mataimakin tsohon kocin tawagar ta Nijeriya, Genort Rohr wanda ya ajiye aikinsa na horar da tawagar bayan da aka kammala gasar kofin kasashen Afirka da aka kammala kasar Cote de’Voire, AFCON 2023.
Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya, NFF na fatan ganin ta nemo wa tawagar Super Eagles sabon mai horaswa domin ci gaba daga inda tsohon kocin mai murabus, Rohr ya tsaya.
Nijeriya da kasar Mali zasu buga wani wasan sada zumunta a tsakaninsu a mako mai zuwa a kasar Maroko kafin ta buga wasa tsakaninta da kasar Ghana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp