Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya shugabanci taron majalisar gudanarwar kasar Sin a yau Litinin, inda aka nazarci tunanin dake kunshe a jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping, yayin taron ayyukan tattalin arziki na kwamitin tsakiya na kasar Sin, kana ya gabatar da shirin aiwatar da manufofin da aka cimma a gun taron ayyukan tattalin arzikin.
A gun taron, an gabatar da shirin kyautata tsarin kula da takardun basussuka na musamman na kananan gwamnatocin kasar Sin, inda aka dauki matakan daidaita jerin sunayen ayyukan da bai kamata kananan gwamnatocin kasar su ba da basussuka gare su ba, da fadada fannonin da ake yin amfani da jarin ayyukan.
Haka zalika kuma, an yi nazari kan yadda za a sa kaimi ga daukar matakan samun bunkasuwa mai inganci, ta amfani da kudin da gwamnatoci suka zuba. An ce ya kamata a kafa tsarin kula da ayyuka bisa kimiyya da fasaha, da yin amfani da kudin da gwamnatoci suka zuba bisa ka’idojin kasuwanci, da dokoki yadda ya kamata. (Zainab Zhang)