Firaministan kasar Grenada, Dickon Mitchell ya bayyana a cikin wata hira da manema labaran CMG a kasar Sin kwanan baya cewa, a cikin ‘yan shekarun nan, tsare-tsaren raya kasa da kasa da kasar Sin ta bullo da su, da dabarun tabbatar da tsaro a duniya, da tsare-tsaren inganta wayewar kai a duniya sun ba da taimako ga ci gaban duniya.
Kana ya bayyana cewa, suna fatan sauran mambobin al’ummomin duniya, musamman na kasashe masu tasowa, za su ba da goyon baya ga wadannan tsare-tsaren. Saboda suna daukar wadannan tsare-tsare a matsayin ka’idoji, da za su iya samar da kyakkyawan tsarin kasa da kasa da zai taimaka musu wajen magance dimbin kalubalen da ke fuskantar duniya a yau yadda ya kamata.
Dickon Mitchell ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa kasashen ta fuskar warware rikice-rikice, da tunkarar batutuwa masu tsanani. Kuma duniya tana bukatar irin wannan jagorancin amma ba babakere ko tattare komai wuri daya ba tare da amincewar saura ba.
Ya kuma kara da cewa, ta hanyar hadin gwiwar shirin Ziri Daya da Hanya Daya, tare da goyon bayan gwamnati da jama’ar kasar Sin, Grenada ta yi nasarar gyara filin jiragen samanta na asali, tare da kammala wasu muhimman gyare-gyare. Saboda Grenada ta dogara kacokan a kan yawon bude ido, don haka yana da muhimmanci a gare ta ta sami filin jiragen sama na duniya na zamani wanda zai iya tallafa wa bunkasa sha’aninta na yawon bude ido. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)