Kwanan nan ne firaministan kasar Kambodiya, Samdech Hun Sen, ya zanta da ‘yar jaridar CMG, inda ya yi fashin baki kan abubuwan da wasu kasashe kalilan suke yi, na matsawa sauran kasashe lamba ko sanya musu takunkumai, ko kuma nuna ra’ayin bangaranci da sauransu, yana mai cewa, takunkumai da ake sanyawa babu kakkautawa, na kara haifar da tashe-tashen hankali a fadin duniya.
A cewar firaministan, kasa da kasa na fuskantar matsalar tsawwalar farashin kayayyaki, kuma rikicin tattalin arziki na faruwa a halin yanzu, ciki har da karuwar farashin man fetur, da matsalar karancin makamashi da abinci. Ya ce kasashen da ake sanyawa takunkumai, suna jin radadi a jikin su, har ma da wadanda suka sanya takunkuman. Ya ce, idan an dauki kasashen Turai a matsayin misali, wadanda ke fama da matsanancin sanyi a halin yanzu, ana iya ganin cewa, suna amfani da kwal ko sare bishiyoyi don dafa abinci, sakamakon rashin makamashin iskar gas. Kuma da wannan yanayi, ta yaya za a aiwatar da yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi da zummar rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli? Ya ce ya kamata wadannan kasashe su waiwayi abubuwan da suka yi, wato kakaba takunkumai, wadanda suka saba da ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban a duniya, gami da ka’idojin kungiyar WTO. (Murtala Zhang)