ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, July 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dabbobin Da Ba Za Mu Kara Gani Ba, Da Masu Sake Dawowa Duniya

by Rabi'u Ali Indabawa
3 years ago
Duniya

Wasu lokutan mu kan yi tunanin da wuya abin da ya shude ya dawo, musamman tabbatar samuwarsa, amma hakan ka iya faruwa.

Kamar yadda gidauniyar kare hakkin dabbobi ta tabbatar, a kowacce shekara sama da tsirrai da tsuntsaye 10,000 ne ke bacewa a doron kasa.

Hukumar ta ce zai yi wuya a tabbatar da ainahin adadi sai dai hasashe, saboda rashin sanin adadin tsirrai da tsuntsayen da ke wurin da ake bincike a kai ba.

ADVERTISEMENT

Yayin da ake gab da fara bikin tunawa da abubuwan da suka bace a ban kasa a ranar 30 ga watan nan, za mu yi waiwaye da duba kan rayuwar wasu daga cikin dabbobi da suka yi rayuwa a baya, amma a yanzu babu su.

An yi amanna da cewa wani nau’in birin ya rayu a duniya tun shekaru 2000 da suka wuce.

LABARAI MASU NASABA

Birtaniya Ta Yaba Wa Tinubu Kan Sauye-sauyen Tattalin Arziki

Jihohi 28 Da Abuja Na Fuskantar Hadarin Ambaliyar Ruwa —Rahoto

Ana yi wa birin lakabi da Mis Waldron Red Colobus, da ke rayuwa tsakanin iyakokin Ghana da Ibory Coast, sai dai ana ganin cewa birin ya bace tun a farkon shekarun 2000.

Birin wanda aka fi samun sa a kan iyakar Ghana da Ibory Coast, na da banbanci da birrai ta hanyar rashin babban dan yatsan hannu.

Dabbace mai nutsuwa da ke rayuwa cikin kungiya tare da darewa saman bishiya, an tirsasa wa birrai zama a ban kasa a lokacin da bil’adam suka fara sare bishiyoyi.
Yayin da dazukanmu ke kara tsukewa, su ma nau’in birin suka fara raguwa, rashin haifarsu da yawa ta hanyar hada aure ya taimaka wajen bacewarsu.

Nau’in kifin Dolphin da ake samu a kogin Yangtze na China
A shekarar 2006 ne China ta nuna nau’in kifin dolphin da take da shi a Kogin Yangtze, ya banbanta da sauran ‘yan uwansa da muka saba gani wanda jikinsu baki ne sidik mai kyalli da santsi musamman idan suna ninkaya a kwami.

Shi wannan nau’in jikin shi ruwan toka ne, ba ya kyalli amma kuma akwai santsi a jikinsa.
Yana da tsawo sosai, an fi ajiye shi a wuri mai amsa kuwwa. Babban abin da ya kara banbanta su da sauran shi ne yana iya gano kifi komai nisan inda yake idan dai cikin ruwa guda suke.

Sai dai kash, yana fuskantar barazanar karewa, saboda kwale-kwale da manyan jiragen ruwa da ke kara-kaina a Kogin Yangtze, da tarkacen abubuwan da ke gurbata muhalla da ake jibgawa cikin kogin.
Yana cikin hadari saboda rashin sabo da sauyin da ya kawo masa ziyara lokaci guda.

Dabbar monk seal (da ake samu tsakanin kasashen Jamaica da Nicaragua)
An fi samun wannan nau’in dabba ta ta Seals Pup a Kogin Medico, da gabar tekunan gabashin tsakiyar Amurka, da tekun arewacin kudancin Amurka.

Sai dai suna fuskantar barazanar karewa, saboda yadda ake farautarsu don jikinsu makare yake da mai, sannan suna mutuwa sakamakon kame abincinsu wato kifaye da ake yi.

Tun daga shekarar 1952 suke ja da baya, kuma an fi samunsu a Yammacin Serranilla tsakanin kasashen Jamaica da Nicaragua.

Dabbar ruwa Alabama Pigtoe (da ake samu a Amurka)
Wannan nau’in dabbar ruwan ta mussel na rayuwa a Tekun Alabama, a Amurka har zuwa shekarar 2006.

An sanya masa sunan ne sakamakon kamanni da kafar Alade, abubuwan da ake sanyawa cikin tekunanmu da ke gurbata muhalli na kashe su, don haka ake ganin kamar ba za su yi tsawon rai a duniya ba.
Shafewarsu a ban kasa na nufin hadarin da tekunanmu ke ciki sakamakon gurbacewarsa, sakamakon sinadarai masu hadari da masana’antu ke zubawa yana kara ta’azzara rashin lafiya ga mazauna kusa da irin tekunan.

Dodo (da ake samu a Kasar Mauritius)
Abu ne banbarakwai a ce an girmama tsuntsu, amma saboda wasu dalilai tsuntsun dodo na daga cikin wadanda suka dade da shudewa a ban kasa ba ya ga dabbar Dinosaurs wacce kusan kowa ya san da ita.
Shekaru aru-aru doguwar tsuntsuwar mai kama da agwagwa ta taba rayuwa a tsuburin kasar Mauritius, ba tare da dogaro wata nau’in dabba ko tsuntsu ba a matsayin abinci.

Bayan bil’adama sun fara zama Mauritius, sun taho da dabbobi daban-daban da sauran nau’in abinci don haka dodo ba ta dade a kasar ba.
Tsuntsun dodo na karshe da aka gani shi ne a shekarar 1700.

Dabbar ruwa Steller’s Sea Cow (An fi ganinta a Alaska da Rasha)
Da kun taba cin karo da dabbar ruwa mai suna Steller’s Sea Cow da kuwa kun san abubuwa da dama akanta.

Jikinta na yanayi da kifi tarwada ne, kuma tana da nutsuwa idan tana tafiya cikin ruwa, amma fa katuwar gaske ce. Bincike da bayanan da aka tattara sun nuna tana da girma da tsawon mita tara.

Ita ma jikinta makare yake da maiko da lallausan nama, watakila shi ne dalilin da rayuwarta ta zama cikin hadari saboda farautarta da ake yi.

Namanta yana da dandanon jan nama da ka jika shi cikin kayan hadi da man almond.
Yawan sauyin abinci, da farauta hadi da gurbacewar muhalli na daga cikin abin da ya janyo bacewar Teller Sea Cow kamar yadda ya faru da tsuntsun dodo.

Dabbar Kuagga (da ake samu a Afirka Ta Kudu)
Kyawun da tsohuwar dabbar Kuagga ke da shi abin kallo ne.
Wannan dabbar da aka fi samunta a nahiyar Afirka, tana da wasu zane-zane kwatankwacin irin zanen jikin jakin dawa mai launin fari da ruwan kasa.
Masu farautar namun daji da kwarjinin dabbar ke daukar hankali ne suka taimaka wajen bacewarta a ban kasa a shekarar 1880 ne aka yi mata ganin karshe.

Kanki na (Ireland)
Yawancin dabbobi ko tsirrai ko tsuntsaye suna kama ko yanayi da juna, amma wasu lokutan ba sosai ba. Wannan nau’in gwankin ana samunsa ne a kasashen Turai.
Kamar dabbar Mammoth mai yanayi da giwa, kama daga haure har girma da zungureren hancin, abin da ya banbanta su shi ne jikinta cike yake da gashi mai tsawon gaske.
Ta shafe a ban kasa shekararu 7,700 da suka wuce, watakil saboda sauyin yanayi da farauta.

Farar mikiya mai doguwar jela ‘yar Birtaniya
A farkon karni na 20 ne farar mikiyar ta bace a Birtaniya, amma ba ta dade ba ta sake dawowa.

Wannan mashahuriyar tsuntsuwar, tana da manyan fuka-fukai masu tsawon sama da mita biyu. Shekaru da dama akai ta farautarta a Birtaniya, kai ba farauta kadai ba har da kisan gilla kuma hakan haramun ne.
A lokacin da aka auna haramcin farautar farar mikiyar, lokaci ya kure don kuwa ta ma kusan karewa.

Amma tana rayuwa a wasu kasashen Turai, kuma watakil ta sake komawa Birtaniya.
Sai dai ba kowacce dabba ce ke samun dama irin ta farar mikiya mai doguwar jela ba.
Mun ciro muku daga BBC

Duniya
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Birtaniya Ta Yaba Wa Tinubu Kan Sauye-sauyen Tattalin Arziki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Kungiya Ta Nemi Mambobinta Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihohi 28 Da Abuja Na Fuskantar Hadarin Ambaliyar Ruwa —Rahoto
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Jami’an Tsaro Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda A Wasu Jihohin Nijeriya, Sun Kama ‘Yan Kasar Pakistan Bakwai

MASU ALAKA

Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Rahotonni

Birtaniya Ta Yaba Wa Tinubu Kan Sauye-sauyen Tattalin Arziki

July 25, 2026
Kogin Kumadugu Ya Yi Ambaliya Karon Farko Cikin Shekara 100 A Yobe
Rahotonni

Jihohi 28 Da Abuja Na Fuskantar Hadarin Ambaliyar Ruwa —Rahoto

July 25, 2026
NLC Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Yajin Aiki Kan Albashi Mafi Karanci
Rahotonni

NLC Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Yajin Aiki Kan Albashi Mafi Karanci

July 24, 2026
Next Post
Real Madrid Ta Lashe Kofin ‘Club World Cup’ Karo Na 5

Real Madrid Ta Lashe Kofin 'Club World Cup' Karo Na 5

LABARAI MASU NASABA

Duniya

Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Naɗa Sabon Mai Ba Shi Shawara

July 26, 2026
Sin Ta Ayyana Shirin Ko-ta-kwana Na Samar Da Tallafin Gaggawa Ga Lardin Guangdong

Sin Ta Ayyana Shirin Ko-ta-kwana Na Samar Da Tallafin Gaggawa Ga Lardin Guangdong

July 26, 2026
Fina-finan Kasar Sin Suna Haskakawa Tare Da Samar Da Dimbin Kudaden Shiga A Zangon Nuna Fina-finai Na Lokacin Zafi Na Bana

Fina-finan Kasar Sin Suna Haskakawa Tare Da Samar Da Dimbin Kudaden Shiga A Zangon Nuna Fina-finai Na Lokacin Zafi Na Bana

July 26, 2026
Shugaban Senegal Ya Jinjinawa Kasar Sin Bisa Taimakon Gina Zaurukan Gudanar Da Wasannin Gasar Olympics Ta Matasa

Shugaban Senegal Ya Jinjinawa Kasar Sin Bisa Taimakon Gina Zaurukan Gudanar Da Wasannin Gasar Olympics Ta Matasa

July 26, 2026
Duniya

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Alƙalin Babbar Kotu A Kebbi

July 26, 2026
Bala Mohammed

Sadakin Budurwa ₦3,000 Na Bazawara ₦1,500: Gwamnatin Bauchi Ta Ƙaryata Batun

July 26, 2026
Arewa Ta Rasa Alƙiblarta – Dattawan Arewa

Arewa Ta Rasa Alƙiblarta – Dattawan Arewa

July 26, 2026
Dauda Dauda Lawal Ya Sha Alwashin Farfaɗo Da Masana’antar Yadi Ta Zamfara

Dauda Dauda Lawal Ya Sha Alwashin Farfaɗo Da Masana’antar Yadi Ta Zamfara

July 26, 2026
Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Kyauta Ga Manoma 150,000  A Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Kyauta Ga Manoma 150,000 A Kaduna

July 26, 2026
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Birtaniya Ta Yaba Wa Tinubu Kan Sauye-sauyen Tattalin Arziki

July 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.