Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce ya kamata a yi kokarin aiwatar da ka’idojin taron koli na raya tattalin arziki tare da kokarin samun sabbin nasarori a fannin ci gaba mai inganci.
Li Qiang wanda kuma mamba ne na kwamitin dindindin na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, ya bayyana haka ne yayin da yake rangadi a lardin Zhejiang daga ranar Laraba zuwa jiya Juma’a.
- Tsarin Tinubu Kan Raya Albarkatun Kiwo Da Samar Da Abinci Yana Haifar Da Ɗa Mai Ido – Minista
- An Bude Sabon Babi A Yankin Macao Wajen Aiwatar Da Manufar Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu A Cikin Shekaru 25
Firaministan ya kuma bukaci a yi aiki tukuru wajen gudanar da bincike kan muhimman fasahohi masu amfanawa bangarori daban daban da kara himmantuwa wajen tsarawa da gina sabbin ababen more rayuwa kamar kumfutoci masu saurin aiki da kara kirkiro sabbin abubuwan da za su zama jagorori a bangarorinsu.
Ya ce, wajibi ne kamfanoni su kara zuba jari wajen bincike da samar da abubuwa da fadada amfani da sabbin fasahohi da sabbin kayayyaki da fadada masana’antu masu tasowa da masu kyakkyawar makoma da kuma samar da sabbin abubuwan da za su ingiza ci gaba.
Ya kuma bayyana muhimmancin karfafawa tsoffin kamfanoni gwiwa ta hanyar sabbin fasahohi kamar na dijital da masu kare muhalli, domin samun damar komawa ga amfani da fasahohin zamani ba tare da matsala ba.
Har ila yau, ya ce ya kamata a gaggauta aikin gina tsarin jigila da na sufuri tsakanin Sin da kasashen waje, da mara baya ga raya harkokin cinikayya da ketare da fadada bude kofa. (Fa’iza Mustapha)