Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gana da ministar kula da harkokin waje da Turai ta kasar Faransa Catherine Colonna, jiya Juma’a a birnin Beijing.
Yayin ganawar, Li Qiang ya ce, tun bayan kulla huldar diflomasiyya a tsakaninsu, Sin da Faransa sun kasance masu girmama juna da tabbatar da daidaito a tsakaninsu, abubuwan dake da muhimmanci sosai ga huldar kasashen 2.
- Masana Sun Yi Gargadi Kan Amfani Da Wani Sinadarin Gishiri A Nijeriya
- Ya Zuwa Karshen Shekarar Bara Tsayin Manyan Titunan Mota Na Kasar Sin Ya Kai Kilomita 177,000
Ya ce, ya kamata bangarorin biyu su ci gaba da mutunta juna da aminci da juna, kana su hada hannu domin samun moriyar juna da ci gaba da karfafa musaya a tsakaninsu da martaba muradun juna da batutuwan dake ci musu tuwo a kwarya, haka kuma su ci gaba da aiwatar da muhimmiyar hulda dake tsakaninsu a dukkan fannoni.
A nata bangare, Catherine Colonna, ta ce a shirye Faransa take ta kara matsa kaimi wajen inganta musaya a tsakaninsu da karfafa amincin siyasa da musaya da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da al’adu da sauran fannoni.
Ta ce, Faransa za ta ci gaba da bude kasuwarta da hada hannu da kasar Sin wajen tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta kamar sauyin yanayi da kare halittu da muhallinsu domin taka rawa wajen kare zaman lafiya a duniya da samun ci gaba na bai daya.
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi da Catherine Colonna sun jagoranci taro karo na 6 na tattauna tsarin musaya tsakanin al’ummominsu, wanda ya gudana jiya Juma’a a nan birnin Beijing.
Bangarorin biyu sun amince su aiwatar da muhimmiyar matsaya da shugabannin kasashen suka cimma da daukar cikarsu shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya da ma shekarar al’adu da yawon bude ido ta Sin da Faransa, a matsayin wata dama ta inganta musaya da samar da karin kuzari da sakamako a dangantakarsu. (Fa’iza Mustapha)