A kwanakin baya, firaministan kasar Pakistan Anwaar-ul-Haq Kakar ya bayyanawa wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG cewa, shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya ta bayyana halinta na musamman idan aka kwatanta ta da sauran tsarukan da suka shafi bangarori daban daban.
Firaministan ya bayyana cewa, abin da ya sanya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya zama ta musamman shi ne ana dogaro da hanyoyin sarrafa tattalin arziki maimakon dogaro da karfin soja don canja duniya. Kasar Sin ba ta son neman sauran kasashen duniya wadanda su da kasar Sin suke yanki daya, ko a duk fadin duniya, da su amince da al’adunta kawai ta hanyar bunkasa shawarar “ziri daya da hanya daya”.
Firaminista ya kara da cewa, ya kamata a bi ra’ayin bude kofa ga mabanbanta tsarukan tattalin arziki da siyasa na sassa daban daban na duniya, sabo da wadannan tsaruka suna da dacewa da al’adun sassa daban daban. Tsarin siyasa ya kasance ba kamar wata rigar da kowa ya iya sanya ba, ya kamata tsarin siyasa ya dace da yanayin da kasa da kasa suke ciki, sakamakon haka, a ganin firaministan, ana iya daidaita matsaloli daban daban ta hanya mafi dacewa bisa hakikanin halin da ake ciki a wurare ko yankuna har ma a duk duniya baki daya. (Zainab Zhang)