A kwanakin baya, firaministan kasar Pakistan Muhammad Shahbaz Sharif ya yi hira da wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping shugaba ne mai hangen nesa, wanda ya jagoranci dukkan kasar Sin wajen cimma burin kyautata tsarin tattalin arziki, kana kasar Sin kasa ce ta biyu mafi ci gaban tattalin arzikin duniya, kana tana daya daga cikin manyan kasashe masu karfin soja a duniya, wadda take kokarin koyar da fasahohin ci gabanta zuwa ga kasashe marasa ci gaba a duniya. Shugaba Xi ya yi kokarin bayar da kira don sa kaimi ga kasashe marasa samun kudin shiga da su iya samu moriya, da samar da dama ga jama’ar wasu kasashe da su cimma nasarar yaki da talauci da more moriyar aikin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama.
Firaminista Shahbaz ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping ya kiyaye tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama, wanda ya bambanta da wasu shugabanni masu ra’ayin kin amincewa da saura. Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya da shugaba Xi ya gabatar tana da hangen nesa, wadda ta sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, da samar da guraben aiki ga kasar Sin da kasashen da ke makwabta da ita da kuma duk duniya baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp