Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa da kasashen Zambiya da Tanzaniya domin bunkasa samun ci gaba a sassan da layin dogo da ke tsakanin Tanzaniya da Zambiya ya ratsa, da kuma hadin gwiwa wajen samar da wata sabuwar cibiyar habaka tattalin arziki.
Ya bayyana hakan ne a birnin Lusaka na kasar Zambiya, yayin da yake halartar bikin kaddamar da aikin farfado da layin dogo tsakanin Tanzaniya da Zambiya, tare da shugaban kasar Zambiya Hakainde Hichilema, da kuma mataimakin shugaban kasar Tanzaniya Emmanuel Nchimbi.
Yayin da yake nuni da cewa, gwamnatocin kasashen uku za su ba da goyon bayan da ya dace don farfado da layin dogon, Li ya bukaci bangarorin uku da su tsaya tsayin daka wajen ganin an gudanar da ayyukan gine-gine masu inganci, da tabbatar da ganin aikin ya cimma matsayin inganci a matakin koli, da zama amintacce abin dogaro, da kuma bayar da misali na hadin gwiwa mai inganci sosai a bangaren shawarar ziri daya da hanya daya.
Firaministan ya kuma kara da cewa, kasar Sin ta kimtsa tsaf wajen hada kai da kasashen Zambiya, da Tanzaniya da sauran kasashen Afirka, wajen ci gaba da aiki da ruhin shirin TAZARA, da aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) na birnin Beijing, da zurfafawa tare da karfafa gina al’ummomin kasashen Sin da Afirka a dukkan fannoni da ke da kyakkyawar makoma a sabon zamani.
A nasu bangaren, Hichilema da Nchimbi sun bayyana cewa, farfado da layin dogon ya sake jaddada makoma ta bai-daya a tsakanin kasashen uku, da kokarinsu na hada karfi-da-karfe domin gina kyakkyawar makoma, kana suka ce layin dogon zai kasance wani kyakkyawan misali na zahiri a kan yadda jama’ar Sin da Afirka ke ci gaba da sada zumunci da yin aiki tare domin sake farfado da ci gaba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














