Firaministan kasar Sin Li Qiang ya yi kiran hada karfi da karfe domin tabbatar da kyakkyawar aiwatar da manufofin gwamnati da kuma fara harkokin bunkasa tattalin arziki na wannan sabuwar shekarar ta 2025 da kafar dama.
Ya yi kiran ne yayin da yake rangadi a birnin Jinan da ke lardin Shandong na gabashin kasar Sin.
- Tabbas Sin Za Ta Ci Gaba Da Jan Zarenta A 2025
- An Yi Taron Ƙungiyar Baburawa Na Abuja Cikin Annashuwa
Da yake kewaya wurare lokacin rangadin a ranar Alhamis din nan, Li ya jaddada bukatar hada karfi wuri guda wajen aiwatar da manufofin gwamnati ba tare da bata lokaci ba, da kiran kara saurin ci gaban da ake samu na gudanar da ayyukan raya kasa tare da tabbatar da cewa kwalliya na biyan kudin sabulu.
Har ila yau, Li ya ziyarci tashar caji da sauya baturan ababen hawa na lantarki da ke Jinan, inda ya yi nuni da cewa, adadin motoci masu amfani da sabon makamashi na ci gaba da karuwa a kasar Sin, sai ya yi kiran kara azamar bullo da sabbin kirkire-kirkire a bangaren aikace-aikacen cajin batura da sauya su da kuma sauran ayyukan da suka jibinci sashen. (Abdulrazaq Yahuza Jere)