Sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC daga jihar Kano ta samu nasararta ta farko a gasar Firimiyar ta Nijeriya (NPFL) bayan doke Kun Khalifa daga jihar Imo a wasan mako na 5 da aka buga a birnin Aba. Wannan shi ne karon farko da ƙungiyar ta samu nasara tun bayan haurowarta gasar.
A minti na 14 da fara wasan ne Kun Khalifa suka fara zura ƙwallo a ragar Barau FC. Sai dai minti biyu kacal bayan haka, Yahaya Ibrahim ya farke wa Barau FC kwallo, wanda ya buɗe musu ƙofar dawowa cikin wasan.
- Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril Ya Yi Alhinin Rasuwar Buhari
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Hillary Ekawu ya ƙara ƙwallo ta biyu ga Barau FC kafin Yahaya Ibrahim ya sake zura ƙwallonsa ta biyu a wasan, wadda ta zama ta uku ga Barau FC, domin tabbatar da cikakkiyar nasara.
Da wannan sakamako, Barau FC yanzu na da maki 5 a teburi, inda ta samu nasara sau ɗaya, aka doke ta sau biyu, sannan aka tashi kunnen doki sau biyu daga cikin wasanni biyar da ta buga. Wannan nasara ta baiwa ƙungiyar ƙwarin gwuiwa yayin da gasar ke ci gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp