Da yammacin nan ne aka samu labarin rasuwar fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Malam Umar Yahaya Malumfashi.
Marigayin ya kasance fitaccen jarumi da ya taka rawa a fina-finan Hausa da dama ciki har da shirin nan mai dogon zango da ake haskawa a gidan Talabijin na Arewa24, Kwana Casa’in.
Ya rasu ne a yau Talata bayan ya yi fama da jinya.
Ko a makon jiya sai da aka yi masa hasashen mutuwa wanda daga bisani ya fito ya karyata, kana ya nemi a taya shi da addu’a.
Daya daga cikin masu harkar fim, Nasiru Sa’ad Gwangwazo wanda har ila yau shi ne Editan Jaridar Blueprint Manhaja, ya wallafa ta’aziyyar rasuwar marigayin a shafinsa na facebook wanda yake kara tabbatar da labarin rasuwarsa.
Shi ma da yake ta’aziyyar marigayin, fitaccen marubuci kuma mai shirya fina-finai, Maje El-Hajeej ya bayyana cewa,
“RAI BAKON DUNIYA…. Mazauna unguwar Hotoro sun tabbatar da cewa, yana ɗaya daga cikin masu kiyaye Sallah a cikin sahu. Kusan kowacce Sallah a cikin jam’i yake yi. Ko lokacin Boko Haram yana daga cikin ‘yan kwamitin Masallaci da suka rika koya wa mutane dabarun kare kai daga hare-haren ta’addanci.
“Mutum mai mu’anala da mutane tare da haƙuri yayin da ka kira shi aiki. Allah Ya jikanka Ya gafarta maka.”
Malam Umar Yahaya Malumfashi dai an fi sanin sa da sunan “Ka Fi Gwamna” a kwanan nan saboda shirin Kwana Casa’in.