Allah Ya yi wa fitaccen malamin Addinin Musulunci Dokta Muhammad Ibrahim Hafiz Ismail Surty rasuwa.
An bayyana shi a matsayin uba, masoyi, kaka, kuma babban malami, a wata sanarwa da Bashir Gwandu ya fitar a Abuja ranar Laraba.
- Sojojin Nijar Sun Tir Da Takunkuman Da ECOWAS Ta Sanya Musu
- Yanzu-Yanzu NLC Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Shiga
Sanarwar ta ce rasuwar Dokta Surty ta sa masoyansa da sauran al’umma cikin jimami.
Dokta Surty ya kasance mutum da ake girmama shi sosai saboda yanayin tausayinsa da yanayin tafiyar da rayuwarsa.
Ya kasance yana jagorantar sallah a babban masallacin Birmingham da kuma Masallacin Jami’ar Birmingham.
Ya kuma kasance Farfesa a Jami’ar Birmingham.
A nan Nijeriya, shi ne mai gabatar da shahararren shirin talabijin mai suna ‘Hasken Musulunci’.
Ya kuma kasance yana aiki a gidan talabijin na Sakkwato a shekarun 1980.
Za a yi jana’izarsa da misalin karfe 1:45 na rana a babban masallacin Birmingham da ke lamba 180 Belgrave Middleway a Ingila.