Fitaccen Malamin Musulunci mai da’awar Sunnah a Nijeriya, Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi da ke jihar Bauchi a Nijeriya ya rasu, malamain ya rasu bayan ya sha fama da rashin lafiya ta tsawon lokaci.
Sheikh Idris wanda shi ne babban limamin masallacin juma’a na Dutsen Tanshi, ya rasu a jihar Bauchi bayan dawowarsa daga ƙasar Indiya, inda ya yi jinyar rashin lafiya a can.
- Rundunar ‘Yansanda Ta Shelanta Neman Dakta Idris Dutsen Tanshi Ruwa A Jallo
- Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Tasa Keyar Dakta Idris Dutsen Tanshi Zuwa Gidan Yari
Rahotanni sun bayyana cewa, malamin ya ɗauki lokaci mai tsawo ya na fama da rashin lafiyar, kuma a wasu lokutan yana zuwa jinya, ya dawo ya ci gaba da koyarwa kamar yadda ya saba.
Daga daga cikin almajiran malamin na kusa-kusa, Abdulhakeem Shaaban Baban Keke, ya tabbatar da rasuwar malamin zantawarsa da LEADERSHIP HAUSA cikin daren ranar Alhamis.
Shaaban, ya ce malamin ya rasu ne a Bauchi bayan ya dawo daga jinya a ƙasar Indiya, a sakamakon rashin lafiyar ne ma bai samu gudanar da wa’azi a watan Ramadana da ya gabata ba, sannan bai samu jagorantar sallar Idi na bana kamar yadda ya saba a kowacce shekara.
Ana yi wa Shehin Malamin laƙabi da Dr. Tauhidi saboda da’awarsa ta ƙarfafa ne akan Tauhidi da kuma riƙo da Sunnar Annabi (S.A.W.) da kuma yaƙi da fararrun al’amura a cikin addinin Islama.
Za a yi sallar jana’izar Babban Limamin da misalin ƙarfe 10 na safe a Masallacin Idi na Games Village, Jihar Bauchi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp