ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Tasa Keyar Dakta Idris Dutsen Tanshi Zuwa Gidan Yari

by Sabo Ahmad
3 years ago
Dutsen Tanshi

Kotu ta aike da fitaccen malamin addinin a Jihar Bauchi, Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi gidan yari bisa zarginsa kalaman tada zaune tsaye da ke barazana ga zaman lafiya.

Malamin wanda ya amsa gayyatar ‘yansanda a ranar Litinin daga bisani suka gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin tada zaune tsaye.

  • Wasan Dambe: Dogon Dan Ladi Ya Doke Autan Kudawa
  • Shugaban EFCC Ya Nemi Cin Hancin $2m A Wajena, Ina Da Hujja –Matawalle

Bayanan da ke zuwa mana na cewa ‘yansandan sun gurfanar da shi ne a gaban kotun Majistire ta 1.

ADVERTISEMENT

Kotun ta tura shi zuwa gidan yarin kafin daga bisani a cigaba da sauraron karar da ‘yansanda suka shigar da shi a ranar Talata.

Da yake tabbatar da kamun da aka yi wa malamin, Shugaban kungiyar, Majalisar Matasa Masu Neman Hadin Kan Malamai Da Cigaban Al’ummar Jihar Bauchi, Yusuf A. Jibrin, ya bayyana cewar malamin ya je wajen ‘yansanda domin amsa gayyatar da suka yi masa ne amma daga bisani suka gurfanar da shi a gaban kotu.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

Ya ce: “Na san da gayyatar da aka yi wa Malam daga hukumar ‘yansanda wanda a ranar Litinin da safe aka tabbatar mana da cewa Malam ya amsa wannan gayyatar.

A da kam ma mun shirya har da ni muka ce za mu je mu yi masa rakiya. Amma da muka yi waya da Allaramma sai ya ce mana a’a malam ya ce bai bukatar kowa ya je. Zai je shi kadai da direba da Malam Ya’u.

“Dazu kuma sai shi Alaramma ya kira ni yake ce min an kai Malam gidan Yari. Yake ce min har an kai shi kotu, kotu kuma ta tura shi gidan yari.”

Yusuf ya ce, dukkanin abin da ake cajin malamin nasu a kai abu ne da ya shafi akidarsu, “Wannan maganar da malam ya yi akidarmu ne a kai kuma muke fatan Allah ya karbi rayukanmu, kuma manufarmu daya kuma a kanta muke.”

A cewarsa, malaminsu ya koyar da su zaman lafiya da kwanciyar hankali, don haka za su bi dukkanin matakan da suka dace a doron shari’a wajen nema wa malaminsu hakkinsa.

Shugaban, ya bayyana cewar su na ta kokarin kwantar wa almajiran malamin hankali da su kwantar da hankalinsu yayin da ake cigaba da bin matakan da suka dace wajen ganin malamin ya samu ‘yanci.

“Muna kira ga mutanenmu da su kasance cikin zaman lafiya kuma za mu bi lamarin a bisa tsarin doka domin mu tabbatar mun bi kadin abin da aka yi mana,” Yusuf A. Jibrin ya shaida.

LEADERSHIP HAUSA ta labarto cewa, a kwanakin baya ne IdrisAbdul’aziz Dutsen Tanshi ya yi furucin cewa ‘…Ko taimakon Manzon Allah ma ba su bukata. Kafin nan ya jero sunayen wasu Shehunnan Darika inda ya nuna cewa ba a neman agajinsu a yayin neman taimako ko a lokacin da ake cikin yanayi na musifa.

Bayan yin jawabin nan nasa ne wasu ke ganin rashin ladabi wajen shigo ga Manzon Allah (SAW) cikin misalinsa wanda kai tsaye wasu suka nuna hakan da rashin kimanta Manzon Allah.

A kan hakan, hukumar shari’a ta Jihar Bauchi ta aike da wasikar gayyata ga Malam Idris domin ya bayyana a gaban malamai domin wanke kansa ko kare kansa sai dai bayan caa da malaman da ke goyan bayansa suka yi hakan ya gagara ba tare da an samu yin wannan mukabalar ba.

Dutsen Tanshi
Sabo Ahmad
+ postsBio
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    An Gurfanar Da Mutum 3 Bisa Laifin Lakada Wa Wani Duka Har Lahira
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    Uwa Ta Mutu A Kokarin Raba Fada Tsakanin ‘Ya’yanta A Abuja
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    ’Yan Fashi Sun Yi Shigar Injiniyoyi, Sun Saci Manyan Na’urorin Sadarwa
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    Ta Sayar Da Jariririyarta Domin Ta Biya Bashin Banki

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
Ba Na Iya Barci Saboda Matsalar Tsaro Lokacin Da Nake Mulki –Jonathan

Ba Na Iya Barci Saboda Matsalar Tsaro Lokacin Da Nake Mulki –Jonathan

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.