Fitacciyar mai yada labarai ta gidan Talabijin ta Nijeriya (NTA), Aisha Bello Mustapha ta rasu.
Aisha, shahararra ce a shirin yada labarai na shirin ‘Network’ da ya ke gudana da misalin karfe 9 na dare. Hajiya Aisha ta rasu ne a safiyar ranar Litinin.
- Kowacce Yarinya Za Ta Samu Ilimi Da Sana’a A Jihar Katsina – Gwamnati
- Don Kare Hakkin Dan Adam Ana Bukatar Gudunmowa Maimakon Takunkumi
Duk da cewa, har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai game da mutuwarta ba, amma dai ta rike matsayin Janar Manaja na Majalisar NTA, kuma ta yi ritaya a watan Mayun 2022.
An bayyana cewa, za a gudanar da sallar jana’izarta da misalin karfe 1:00PM a babban masallacin kasa dake Abuja babban birnin tarayya a yau Litinin.