Gidauniyar Zakka da Wakafi ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa, fitar da zakka da kuma bayar da ita ga wadanda addini ya tanada a bai wa matsayin wata hanya guda ta magance dukkanin wata kofar talauci da ke addabar jama’a.
Sakataren gidauniyar Zakka da Wakafi ta Jihar Kaduna, Malam Nuruddeen Muhajid ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kaduna.
- Kotu Ta Kori Kakakin Majalisar Dokokin Filato
- Kaunar Da Xi Jinping Yake Nuna Wa Gari, Dangi Da Kuma Al’ummar Kasa
Muhajid ya kara da cewa bisa la’akari da halin da jama’ar Musulmi suka tsinci kansu na sakaci da wannan rukuni na bayar da Zakka ne ya sa suka samar da wannan gidauniya wacce take tattarowa gami da rarraba Zakka a tsakanin al’umma kuma ita ce ta farko irinta a Jihar Kaduna.
Sakataren ya kara da cewar sun kafa gidauniyarsu ne tun a shekarar 2021, kuma tun daga wannan lokaci suke aikin tara kudaden Zakka daga hannun masu hannu da shuni.
A cewarsa, a shekarar farko sun raba naira miliyan Uku, sannan a shekara ta biyu suka raba naira miliyan 10, yayin da a shekarar bara suka raba naira miliyan 16.
Ya ce “A farkon shekarar nan mun gudanar da babban taro na kasa domin wayar da kan jama’a a kan muhimmancin bayar da Zakka. Inda muka gayyato jama’a daga dukkanin jihohin kasar nan 36 har da Abuja aka yi babban taro Kaduna wanda kuma an samu nasara sosai.”
Ya bukaci daukacin al’ummar Jihar Kaduna musamman masu hannu da shi da su rika fitar da Zakka domin rage radadin talauci da ya yi al’umma katutu. Ya ce kofar gidauniyarsu a bude take wajen amsar Zakka da Wakafi domin raba su ga wadanda suka dace su samu.