A cikin watanni shida da suka gabata, fiye da mata masu haƙar ma’adinai 50 ne a Jihar Nasarawa suka fuskanci cin zarafi daga abokan aikinsu maza, kamar yadda ƙungiyar Women In Mining In Nigeria (WIMIN) ta bayyana yayin horon kwanaki 3 kan Cin Zarafin Jinsi da Jima’i (SGBV) a Lafia.
WIMIN tare da hadin gwuiwar Ford Foundation, sun nuna ƙaruwar cin zarafin mata da take haƙƙin jinsi a wuraren haƙar ma’adinai, suna kira da a ɗauki matakin gaggawa daga masu ruwa da tsaki don magance wannan matsala.
Shugabar WIMIN, Janet Adeyemi, ta ce kashi 90% na mambobin ƙungiyar a faɗin ƙasa sun fuskanci irin wannan cin zarafi, tana mai jaddada buƙatar ɗaukar matakin bai ɗaya don kare haƙƙin mata a ɓangaren haƙar ma’adinai.
- Karkatar Da Goron Sallah: Ku Dawo Da Kuɗin Ma’aikata Ko Mu Hukunta Ku” – Gwamnan Sakkwato
- Wani Matashi Ya Yi Barazanar Faɗowa Daga Dogon Ƙarfen Gidan Rediyo A Abuja
Mataimakiyar Shugabar WIMIN, Regina Edzuwah, ta yi kira ga masu ba da hidima da masu ruwa da tsaki su jajirce wajen yaki da cin zarafi da muzgunawa a wuraren aiki da al’umma. Adeyemi ta bayyana cewa duk da yawancin kamfen din wayar da kai da aka gudanar, hakkin mata ma’adinai ne mafi cin zarafi da raini.
Horon, wanda aka lakaba “Kawar da Cin Zarafin Jinsi da Jima’i a Al’ummomin Masu Hakar Ma’adinai,” ya yi niyya wajen magance SGBV ta hanyar ilmantar da mahalarta kan batutuwa masu mahimmanci kamar al’adun da ke tasiri ga SGBV, tsarin doka, hanyoyin kula da wadanda suka tsira daga cin zarafi, da kuma kula da raunukan kwakwalwa.
Daraktan kula da kare Jama’a a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Nasarawa, Justina Allu, ta tabbatar da karɓar fiye da ƙorafin SGBV 50 cikin watanni shida da suka gabata. Ta bayyana ƙudirin gwamnati na magance waɗannan laifuka.