Fursunoni guda goma sha ɗaya daga gidan yari mai matsakaicin tsaro a Kaduna sun sami digiri na farko da takardun shaidar babbar Difuloma (PGD) daga Jami’ar NOUN.
Fursunoni bakwai sun kammala da kyakkyawan sakamako mai darajar Upper Second-Class, biyu sun samu Lower Second-Class, yayin da biyu suka sami takardun PGD. Waɗannan fursunoni sun kammala karatunsu ne ta hanyar cibiyar NOUN da ke gidan yari cikin shekaru huɗu zuwa biyar.
- Da Ɗumi-ɗumi: APC Ta Lashe Zaɓen Ƙananan Hukumomin Kaduna
- Da Ɗumi-ɗumi: APC Ta Lashe Zaɓen Ƙananan Hukumomin Kaduna
A lokacin wani ƙaramin bikin yaye fursunonin da aka yi a gidan yari na Kaduna, wakilin Mataimakin Shugaban Jami’ar, Dr. Baba, tare da Shugaban Kula da Gidajen Yari na Jihar Kaduna, Nuru Mohammed Isah, sun miƙa takardun ga fursunonin. Dr. Baba ya yabawa jarumtar fursunonin wajen kammala karatunsu duk da ƙalubalen da suka fuskanta a matsayin waɗanda aka kulle.
Shugaba Isah ya kuma jinjinawa fursunonin bisa ƙoƙarinsu na cimma nasara a fannin karatu duk da ƙalubalen zamantakewa da ke tattare da karatu a gidan yari.
Haka nan, Mataimakin shugaban masu kula da Gidajen Yari, Abdullahi Dangani, ya gode wa NOUN bisa gudunmuwar da ta bayar wajen kyautata halayen fursunonin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp