Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ba zai yiwuwa ba fursunonin da ke gidajen gyaran hali a fadin kasar nan su kada kuri’a a lokacin babban zaben 2023.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana haka a lokacin da tawagar gudanarwar hukumar da ke kula da Gidajen gyaran hali ta Nijeriya ta kai masa ziyara a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Talata, ya jaddada bukatar cimma matsaya guda kafin fursunonin su kada kuri’a.
Da yake karin haske kan lamarin, Yakubu ya bayyana cewa sauran watanni bakwai kacal a gudanar da babban zaben, akwai bukatar lura da tantance hanyoyin da fursunonin za su kada kuri’a, ya ce: “Babban zabe mai zuwa ba shine zaben karshe da Nijeriya za ta gudanar ba.”
Ya kara da cewa, “Don haka ko da ba mu cika dukkan wadannan muhimman matakai na 2023 ba – Wanda zai ba fursunonin damar kada kuria, za mu ci gaba da tattaunawa kan lalubo mafita zuwa zabe na gaba.
“Wadannan batutuwa ne masu Muhimmanci matuka da ya kamata mu tattauna akai sosai.”