Shugabannin kasashe bakwai masu karfin tattalin arzikin masana’antu a duniya (G7), sun lashi takobin ci gaba da marawa Ukraine baya dangane da mamayar da Rasha ta yi mata.
Cikin wata sanarwa da ta fitar yayin taronta a kudancin Jamus, G7 ta ce, za ta ci gaba da bai wa Ukraine tallafin kudi da na jin kai har da na soji da kuma na diflomasiyya tare da tsayawa kafa-da-kada da kasar da yaki ya daidaita.
- An Gudanar Da Dandalin Cibiyoyin Ilimi Na Sin Da Afirka Na Shekarar 2022
- NIS Ta Bi Ƙa’ida Sau Da Ƙafa Wajen Bai Wa David Nwamina Fasfo – CGI Isah Jere
Wannan sakon marawa Ukraine baya na zuwa ne bayan tattaunawar sama da sa’o’i biyu da shugabannin G7 suka yi da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ta bidiyo.
Shugaban Jamus mai masaukin baki Olaf Scholz, ta shafinsa na Twitter ya wallafa goyon bayan kungiyar na tsayawa kai da fata don taimaka wa Ukraine da tuni babban birninta Kiev ya fuskanci farmaki makami mai linzami daga Rasha.
Scholz, ya ce dole su dauki matakai masu tsauri da kuma suka dace, tare da kara matsin lamba kan Putin, don kawo karshen yakin.
Mambobin kungiyar sun gargadi Rasha kan bada damar jigilar kayayyakin abinci ficewa daga Ukraine domin kaucewa ta’azzara matsalar karancin abinci a duniya.
Shugabannin sun kuma yi kira ga Moscow da ta kyale ‘yan kasar Ukraine da aka tilastawa komawa gida nan take cikin aminci.
Kasashe masu arziki sun nuna matukar damuwarsu kan shirin da Rasha ke yi na isar da makamai masu linzami da za su iya daukar nukiliya zuwa Belarus a watanni masu zuwa.
Majiyar G7 ta ce, Zelensky ya bukaci shugabannin kasashen duniya da su yi iyakacin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen mamayar da Rasha ke yi wa kasarsa a karshen wannan shekara, domin yanayin yaki zai kara tsanani ga dakarunsa yayin da suke kokarin kare kasarsu.
Zelensky ya jaddada bukatar ci gaba da daukar tsauraran matakai kan Rasha, da kuma kar a rage matsin lamba duk da takunkumin da kasashen yammacin Turai suka dauka kan Moscow.
Ya ce bai shirya bude tattaunawa da Rasha ba, saboda har yanzu Kyiv na neman karfafa matsayinta, in ji fadar shugaban kasar Faransa.