Matsananciyar gabar da ke tsakanin wasu kungiyoyin ‘yan bindiga da ke a Jihar Zamfara ya kara kamari inda wasu kungiyoyi hudu da suka yukura domin aiwatar da ramuwar gayya.
Wasu majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa, wasu daga cikin kungiyoyin kuma sun yi watsi da yiwuwar kulla yarjejeniyar zaman lafiya a kan sauran, yayin da suke shelanta ci gaba da yin adawa da sauran.
- Sauyin Yanayi: Dabarun Da Za Su Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi
- NDLEA Ta Cafke Mai Ciki Da Kudin Jabu Naira Miliyan 3.2
A ranar Asabar din da ta gabata, 14 ga Afrilu, 2024, wakilan kungiyoyin uku daga cikin hudu – Dan Karami Gwaska da Alhaji Shingi, sun yi taro a Kauyen Usu da ke Karamar Hukumar Birnin-Magaji domin tattaunawa a tsakaninsu. Kungiyar Bello Turji ba ta halarci taron ba.
Ado Aleru ya wakilci kungiyar Alhaji Shingi; Bello Tagoje ya wakilci kungiyar Kachalla Halilu; yayin da Ardo Na-shawari, Alhaji Ali, Alhaji Shamago da dan Karami Gwaska suka wakilci kungiyar Gwaska.
Kungiyar ta Shingi wanda Ado Aleru ya wakilta, ta yi gargadi ga kungiyar Gwaska cewa kada ta sake sanya kafarta a al’ummar Tsanu da Rukudawa na Karamar Hukumar Zurmi. Sun kuma yi gargadin cewa idan Gwaska ya yi watsi da gargadin da suka yi masa, za su kashe shi da wasu daga cikin mutanensa.
A ci gaba da fafatawa da su shugabannin ‘yan bindiga uku, Ado Allero, Dan Yusufa da Mali sun riga sun ajiye mutanensu a Arewacin Tsafe, a shirye-shiryen tunkarar duk wata arangama.
A matsayin wani sharadi na zaman lafiya kuwa, kungiyar ta Shingi ta bukaci Dan Karami Gwaska ya mayar wa wani Hassan shanun da ya sace a Bafashi na Karamar Hukumar Safana ta Jihar Katsina.
Sun kuma bukaci Dan Karami Gwaska ya mayar wa Sani Dangote makaman da ya kwace masa a makon da ya gabata; sannan kuma ya sayi sabbin babura a matsayin diyya ga wadanda ya kona na mutanen Dangote.
Kungiyar Dan Karami Gwaska ta amince da dukkan sharuda.
Sai dai Bello Turji, wanda bai halarci taron ba, ballantana ya tura wakilai, ya yi watsi da yiwuwar samun zaman lafiya tsakaninsa da Gwaska, inda ya tabbatar da cewa zai ci gaba da farautar Gwaska har ya ga bayansa.