• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gamayyar kungiyoyin Seyi Tinubu (STSG) Na Shirin Gangamin Taronta Na Kasa

by Sani Anwar
6 months ago
Seyi

Hon. Sanusi Ibrahim Yaro, Darakta Janar na Gamayyar kungiyoyin Seyi Tinubu na kasa (STSG), ya bayyana cewa; nan ba jimawa ba, za su yi gangamin taronsu na kasa baki-daya.

“Za mu yi wannan gangamin taro ne, domin sake tabbatar da samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu, wanda muke sa ran aiwatar da taron nan da ‘yan wasu makwanni kadan masu zuwa,” in ji Yaro.

  • ‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Na’urorin Zamani Daidai Lokacin Da Sojoji Ke Da Karancin Makamai -Zulum
  • Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jaridar Da Ya Fallasa ‘Sharrin’ Da Ake Shirya Wa Natasha

Ibrahim ya ci gaba da cewa, suna nan suna ci gaba da aiki babu dare babu rana, domin kuwa maganar da ake yi yanzu, dukkanin jihohin Arewacin wannan kasa da wasu daga cikin jihohin kudancin ƙasar nan, na nan suna shirya tarukansu daban-daban, kafin wannan babban taro da za a aiwatar na kasa a babban birnin tarayya Abuja.

“Tunda aka kafa wannan kungiya, ba mu yi kasa a gwiwa ba wajen tallata ayyuka da manufofin wannan gwamnati ga musamman ‘yan’uwanmu matasa maza da mata, don sanin irin kokarin da shugaban kasa ke yi na ciyar da wannan kasa gaba.”

Har ila yau, a cewar Hon. Yaro; sun yi wa wannan ƙungiya lakabi da sunan Seyi Tinubu (STSG) ne, saboda jajircewar Seyi Tinubun a kan matasa maza da mata.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman

Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Zariya

Kazalika ya kara da cewa, idan za a iya tunawa, Seyi ya kewaya kusan dukkanin jihohin Arewacin kasa nan tare da tallafa wa al’umma da kayan abinci da kudade, musamman a watan Ramadana da ya gabata.

A karshe, Sanusi ya yi kira ga matasa maza da mata, kada su bari a bar su a baya a wannan tafiya, domin kuwa kungiya ta kowa da kowa ce, duk mai bukatar yin rajista; kofa a bude take, domin kuwa suna da ofisoshi a kowace jiha, ciki har da babban birnin tarayya Abuja da suke shirin bude kwanan nan ga masu bukatar shiga.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman
Kananan Labarai

Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman

September 26, 2025
Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Zariya
Kananan Labarai

Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Zariya

April 18, 2025
Ƙarin Harajin Amurka Zai Illata Tattalin Arziƙin Duniya
Kananan Labarai

Ƙarin Harajin Amurka Zai Illata Tattalin Arziƙin Duniya

April 5, 2025
Next Post
Ta Yaya Kasashe Masu Tasowa Za Su Iya Tinkarar Yakin Haraji Da Amurka Ta Tayar?

Ta Yaya Kasashe Masu Tasowa Za Su Iya Tinkarar Yakin Haraji Da Amurka Ta Tayar?

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.