Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa da ke Kudancin Nijeriya a Jihar Legas ta yi Allah wadai da yadda hare-haren ta’addanci suke kara tsamari a yankunan arewa.
Gamayyar wacce ta nuna takaicinta kan lamarin ta bakin shugabanta, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci, ta bayyana cewa bisa irin ukubar da ake sha, lokaci ya yi da mutanen arewa za su gane ba su da shugabanni masu kishin su, “domin yadda ake kashe mutane tsakanin Katsina, Sakkwato, Zamfara da Kaduna babu ji babu gani kuma an ja baki an yi shuru abin ya wuce hankali. Shin akwai maganar da wasu za su fada nan gaba mu ji su mu yi aiki da su kuwa?”
“Domin kamar tsuntsu ya fi Dan’adam daraja a Nijeriya musamman wanda ya fito daga yankin arewacin kasar, wato su a tunanin shugabaninmu ba mu san abin da muke yi ba ko? A sace mu a dinga yi mana kisan gilla amma ko a jikinsu muna kira da babbar murya ga masu madafan iko na arewacin kasar nan da su yi karatun ta nutsu saboda duk nisan jifa kasa za ta sauko.
“Tun a 1999 ake yakar arewa ana sace dukiyar da Allah ya shimfida a yankin. A bisa wannan ne ma aka kirkiri boko haram da fadar Fulani makiyaya, ga ‘yan kungiyar aware ta kabilar ibo, ga kungiyoyin yarabawa. Duk wadannan kungiyoyin ba su da wani buri ban da kisan mutanen arewa.” In ji gamayyar.
Wakazalika gamayyar ta ce a halin yanzu abin ya zama wa ‘yan arewa gaba-kura-baya-siyaki saboda ana kashe a yankinsu, sannan yankunan da wasunsu suka fita neman abinci ma ana musu barazana, tana mai cewa, “Ba za mu manta da kalaman da Gwannan Ondo ya yi a kan jama’ar arewacin kasar nan wanda ya ce Hausa/Fulani tarihi yana maimaita kansa, su Sardauna, Tafawa Balewa da Murtala Ramat Muhammed duk kisan gilla aka yi musu, Kun manta da wannan? Dan hakka ku canja tunani saboda lokaci ya kusan kure muku.
Wai a ce daga bakin gwamna ne sukutum wannan maganar ta fito kuma babu mai nuna masa yatsa daga arewar, to ina ake so al’ummarmu ta saka kanta?”