Rahotannin na nuna cewa, wasu da ba a san ko su wanene ba suna shirin jagorantar gudanar da gaggarumar zanga-zanga shigen irin wannan da aka yi shekarun baya mai suna #EndSARS, sun shirya zanga-zangar ne don kalubalantar tsananin tsadar rayuwa da ake fuskanta a Nijeriya. Wadanda suka bayar da wa’adin fara zanga-zangar suna ganin cewa, gwamnatin tarayya ba ta yi abin da ya kamata ba domin maganin matsalar tsadar abinci da ake fuskanta wanda yake neman jefa al’umma cikin halin ni ‘ya su. Mun dauki wannan lamarin da muhimmanci sosai, ya kuma kamata a gaggauta daukar matakin ganin an kawo karshensa.
Masana na da ra’ayin cewa, rikicin ya taso ne sanadiyyar matsalar tsadar abinci tana iya barazana ga tsaron kasa gaba daya. Ba bama-baman nukiliya suka rusa daular gurguzu ta rasha ba. Matsalar tsadar rayuwa ce haifar da juyin juya hali na kasar Faransa. Kuma gashi kasar nan ta yi shekara 15 tana fuskantar yaki da ta’addanci da harkokin ‘yan bindiga. Kara matsalar tsadar abinci a ra’ayinmu, wani abu ne da ba zai haifar wa Nijeriya da da mai ido ba. Matsalar tattalin arzikin da ake ciki ta jefa ‘yan Nijeriya da dama cikin wahalar samun cin abincin yau da kullum a cikin sauki. Harkokin rayuwa suna kara hauhawa a kullum, farashin kayan masarufi, man fetur da wutar lantarki sun yi tashin gwauron zabo, a kullum kuma abin kara tashi suke yi.
- Tsadar Rayuwa: ‘Yan Majalisa Sun Rage Albashinsu Da Kashi 50 Cikin 100
- Zanga-zanga: Minista Ya Nemi Jama’a Su Ƙara Haƙuri, Gwamnati Na Ƙoƙarin Rage Tsadar Rayuwa
A hasashen ta na baya-bayan nan, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, ‘yan Nijeriya fiye da Miliyan 82 kusan kashi 64 na al’ummar kasar za su fuskanci yunwa nan da shekarar 2030. A kan haka ne majalisar ta nemi gwamnati ta dauki matakan dakile dumamar yanayi, barazanar kwari da sauran matsalolin da ke dakile harkar noma a kasar nan. A halin yanzu saura shekara 6 a kai shekarar 2030 amma lallai ya kamata mahukunta su natsu su yi tunani tare da fitar da hanyoyin da za a kauce wa fadawa matsalar yunwa da rashin abinci a kasar nan.
A matsayinmu na gidan jarida, muna kara tunatar da gwamnati nauyin da ke a kanta wanda ya hada da samar da jin dadin rayuwa ga al’umma, wanda hakki ne da tsarin mulkin kasa ya dorawa gwamnati na ta tabbatar da jin dadi da tsaron al’umma ba tare da nuna banbanci ba.
Duk da haka muna kira ga gwamnati da ta yi mai yiwuwa na hana wa duk wata kungiyar hujjar shiga wata zanga-zanga, abin da zai iya jefa kasar matsalar da ya yi kamata da ta #EndSARS. Wanda aka yi shekarun baya mun ga yadda aka yi asarar rayukan mutane aka kuma barnatar da dukiyoyin al’umma. Zuwa yanzu kasar bata farfado daga abin da ya faru a wancan lokacin ba, saboda haka bai kamata a kara jefa amu cikin wata zanga-zangar da zai iya zama mafi muni fiye da na baya ba.
Kwanakin baya, Majalisar Dattawa ta nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta maganin tsadar rayuwa da mastalar abinci da ake fuskanta, ta kuma nemi ta yi wani abu a kan karin kudin wutar lantarki da aka yi don kada a jefa kasar cikin rudanin da zai iya haifar da mastalolin da ba za mu iya dauka ba. Majalisar Dattawa ta sa baki ne ganin abin da ke faruwa a kasar Kenya kwanan nan, inda aka yi wa gwamnati bore saboda karin kudin haraji, inda matasa ke neman a inganta rayuwar al’ummar kasar, sun kuma nemi Shugaban Kasa William Ruto ya yi murabus.
A mastayinmu na gidan jarida, hakki ne a kanmu musamman ganin mune keda hakkin sa ido a kan al’ummuran gwamnati da yadda suke shafar al’umma, mu yi magana domin duk abin da zai faru ya shafe mu a mastayinmu na ‘yan Nijeriya. Muna masu yaba wa gwamnati a kan tallafin tirela 20 da ta bai wa kowace jiha wanda aka shirya raba wa ‘yan Nijeriya fiye da miliyan 163 da ke fuskanta matsalar rashin abinci. Amma wannan tallafin ba zai kai ko ina ba in aka lura da yawan al’ummar da ke fuskantar matsalar rashin abinci.
Kari ga wadancan tileloli na abin da aka tura wa jihohi, ya kamata gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar matakin dawo da tallafin da ta janye a wutar lantarki, man fetur da kuma matsalar rashin daidato na farashin Naira a kasuwannin kasashen waje wanda yake cutar da manya da kananan kamfanoni da kuma al’ummar Nijeriya da ke a kan titunan kasar nan.
A kan haka yana da matukar muhimmanci gwamnati a dukkan matakai su dauki matakai masu muhimmanci na kawo karshen matsalar tsadar raywua da al’umma ke fuskanta. Wannan ba lokaci ne na alkawaurran da ba za a iya cikawa ba, mutane na bukatar a dauki matakin da za su iya gani a kasa ne ba tare da bata lokaci ba.
A kan zanga-zangar tsadar rayuwa da ake shiryawa a fadin Nijeriya, muna kira ga gwamnati da ta dauki matakin yayyafawa shirin ruwa, kada kuma a dauki matakin musgunawa ga matasan da za su fito kan titi domin kuwa lallai al’umma na fama da yunwa, kuma hakki ne na gwamnati ta samar wa al’umma abinci. Lokaci ya yi da gwamnati za ta dauki mataki na kawo karshen matsalolin da al’umma ke fuskanta. Dole gwamnati ta dauki darasi daga gargadin ‘William Shakespeare’ inda ya ce, “Ka yi hankali fushin mai jin yunwa”.