• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gandiroba Ya Hallaka Abokin Aikinsa Kan Abinci A Bauchi

by Sadiq and Khalid Idris Doya
1 year ago
Gandiroba

Wani jami’in hukumar kula da gidajen gyaran hali da ke aiki Burra a ƙaramar hukumar Ningi ta Jihar Bauchi, ya hallaka wani abokin aikinsa sakamakon rashin jituwar da ta ɓarke a tsakaninsu kan abinci. 

Shugaban ƙaramar hukumar Ningi, Hon. Nasiru Zakarai ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a zantawarsa da wakilin LEADERSHIP Hausa ta wayar tarho a ranar Alhamis.

  • Nijeriya Za Ta Haɗa Gwiwa Da Amurka Wajen Inganta ‘Yancin ‘Yan Jarida
  • Asibitin Gombe Ya Haramtawa Ma’aikata Yin Kiripto Lokacin Aiki

Lamarin wanda ya faru a ranar Talata sakamakon cinye abincin abokinsa ya yi, lamarin da ya ja su ga dambarwar kar da gwarin juna da kai.

Wani ganau da dai ya ce marigayin mai suna Aliyu Abubakar Chiroma abokan juna ne da shi wanda ake zargi abokin aikin nasa wato Kabiru Abubakar.

Kamar yadda rahotonnin suka nuna, Kabiru ya cinye wa Chiroma abinci da hujjar Marigayin wani lokaci ba ya yawan cin abincin da ake ba su.

LABARAI MASU NASABA

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

Nasiru ya ce: “Ina jiran cikakken rahoton abun da ya faru daga hukumomin tsaro. Kamar a ɗan bayanin da nake samu ko mutumin Giade ne.”

“Akwai tabbacin faruwar wannan kisar, bayanan da nake samu zuwa yanzu shi ne ko a kan harƙar abincin ne. Dukkaninsu abokan aikin juna ne domin ma’aikatan gidan gyaran hali ne.

“Ka san a na yin abinci na gidan Fursunoni to in an yi a kan ɗan zuba musu su ma su ci. To, shi ne wancan (wanda ya yi kisan) ya ɗauki abincin aikinsa ya ci da domin wai shi marigayin koda an sanya abinci ba yawan ci yake yi ba, sai ya bari ko kwata-kwata ma ba zai ci ba.

“To, sai ya haɗa abincinsa da na wancan don ba wani abinci mai yawa ne cancan ba sai ya ci.

“To, da ya ci sai wancan ya zo yana cewa ina abincinsa, sai ya ce masa kai da ba wani ci kake yi ba, wannan shi ne sanadiyyar faɗan da suka fara doke-doke kawai sai ya gwara kan Marigayin domin ya jawo kansa sai ya gwara da nasa, ka ji abun da ya faru.

“Amma zan binciki cikakken abun da ya faru dags jami’an tsaron kuma zan sanar da kai ƙarin bayanin da na samu daga wanensu.”

Wakilinmu na ta ƙoƙarin samun cikakken ƙarin haske daga hukumomin tsaro a jihar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah
Manyan Labarai

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump
Manyan Labarai

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

November 7, 2025
Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 
Manyan Labarai

Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 

November 7, 2025
Next Post
Bangaren Sin Ya Yi Kira Ga Bangarori Biyu Dake Rikici A Sudan Da Su Yayyafawa Rikicin Kasar Ruwa

Bangaren Sin Ya Yi Kira Ga Bangarori Biyu Dake Rikici A Sudan Da Su Yayyafawa Rikicin Kasar Ruwa

LABARAI MASU NASABA

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri 4, Sun Ƙwato Makamai A Filato

Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

November 7, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

November 7, 2025
GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

November 7, 2025
Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

November 7, 2025
Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.