Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya gabatar da kudirin kasafin kudi na Naira biliyan 245.3 ga majalisar dokokin jihar na shekarar 2023.
A shekarar da ta gabata Ganduje ya gabatar da sama da Naira Biliyan dari da casa’in da shida (N196b) ga majalisar dokokin Jihar Kano, na shekarar 2022.
- Masu Kudaden Haram Za Su Fuskanci Kalubale Da Sauya Fasalin Kudi —Buhari
- 2023: Kungiyar Afenifere Ta Yi Amai Ta Lashe
Kudirin kasafin kudin na shekarar 2023 da aka gabatar yana da biliyan N144.6 a matsayin babbar hanyar kashe kudi wanda ke wakiltar kashi 59 cikin 100 na jimillar kasafin kudin, yayin da kudaden da ake kashewa akai-akai a cikin kudirin da aka gabatar ya kai sama da biliyan 100, wanda ke wakiltar kashi 41 cikin 100 na kasafin.
Kasafin dai shi ne na karshe da Ganduje ya gabatar a gaban majalisar dokokin jihar domin a watan Mayun shekara mai zuwa ne ake sa ran zai kammala wa’adin mulkinsa.