• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ganduje Ya Noƙe Kan Furta Ko Shettima Zai Yi Takara Da Tinubu A 2027

by Abubakar Sulaiman
1 month ago
in Manyan Labarai
0
Ganduje Ya Noƙe Kan Furta Ko Shettima Zai Yi Takara Da Tinubu A 2027
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Wani rikici ya barke a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Arewa maso Gabas da aka gudanar a jihar Gombe, bayan da Mataimakin Shugaban APC na Kasa daga yankin, Comrade Mustapha Salihu, ya amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu don yin takarar wa’adi na biyu ba tare da ambato mataimakinsa ba, Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima ba.

Taron ya samu halartar ministoci, gwamnonin jihohi, da ‘yan majalisar dokoki na jam’iyyar daga yankin. Shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje, ya jagoranci wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa taron.

  • Gwamnan Kano Ya Ceto Dalibai 84 Da Ganduje Yaki Biya Wa Kudin Makaranta A Cyprus
  • Za A Watsa Shirin “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” A Kafofin Watsa Shirye-shiryen Kasashen Tsakiyar Asiya Biyar

Bayan Salihu ya kammala jawabinsa inda ya mara wa Tinubu baya don ya tsaya takara kai tsaye, sai wasu mahalarta suka fusata hayaniya ta barke daga cikin mahalarta taron. Wasu sun fara zagin sa tare da barazanar kai masa hari, inda jami’an tsaro suka yi gaggawar fitar da shi daga dakin taron.

Daily Trust ta rawaito cewa, don kwantar da hankali, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Bukar Dalori, ya fito ya mara wa Tinubu da Shettima baki daya baya don wa’adi na biyu. Sai dai lamarin ya kara rikicewa bayan Ganduje shima ya kammala jawabi ba tare da ambato sunan Shettima ba. Wannan ya sa aka rufe taron cikin gaggawa, yayin da jami’an tsaro suka fitar da Ganduje daga wurin.

Wannan na sake nuna cewa ba lallai Tinubu ya sake takara ta Shettima a matsayin mataimaki ba, wanda kuma hakan zai iya sa wa a samu babbar baraka a cikin jam’iyyar, amma wannan mai sauki ne a wurin manyan jami’an APC domin ana cewa ana su lissafin Shettima ba shi da wani nauyi a siyasance.

Labarai Masu Nasaba

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: APCGandujeShettima
ShareTweetSendShare
Previous Post

Wang Yi Ya Tattauna Ta Wayar Tarho Da Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Isra’ila

Next Post

Ba Zai Manta Da Shawarar Mahaifinsa Ba

Related

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa
Manyan Labarai

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

2 hours ago
Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 
Wasanni

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

18 hours ago
Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson
Siyasa

Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson

23 hours ago
An Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
Manyan Labarai

An Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja

24 hours ago
Gwamnatin Kano Ta Gabatar Da Buƙatu 10 A Gaban Kwamitin Gyaran Tsarin Mulkin Nijeriya
Da ɗumi-ɗuminsa

Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincikar Kwamishinan Sufuri Kan Karɓar Belin Dilan Ƙwaya A Kano

1 day ago
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12
Manyan Labarai

Dangote Ya Ajiye Muƙamin Shugabancin Kamfaninsa Na Siminti

2 days ago
Next Post
Ba Zai Manta Da Shawarar Mahaifinsa Ba

Ba Zai Manta Da Shawarar Mahaifinsa Ba

LABARAI MASU NASABA

Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

July 27, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Wasu Sojojin Bogi 2 A Legas

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yanbindiga Uku Da Kama AK-47 Guda Goma

July 27, 2025
Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

July 27, 2025
Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano

Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano

July 27, 2025
Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu

Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu

July 27, 2025
ADC Ce Za Ta Haɗa Kan Arewa Wajen Kawo Ci Gaba — Mark

ADC Ce Za Ta Haɗa Kan Arewa Wajen Kawo Ci Gaba — Mark

July 27, 2025
Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

July 27, 2025
Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Kaduna Da Zamfara

Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Kaduna Da Zamfara

July 27, 2025
aure

Ko Kin San… Matsalolin Mahaifa Da Suke Hana Haihuwa 

July 27, 2025
VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

July 27, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.