Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya saki adadin fursunoni dubu 3,898 daga gidajen gyara hali daban-daban da suke fadin jihar Kano domin rage cinkso a gidajen yarin a cikin shekaru bakwai da suka wuce.
Aikin sakin daurarrun wanda ya gudana a karkashin kwamitin jiha na afuwa da yafiya da aka sha yi a lokutan bukukuwa musamman irin lokacin Sallah. Fursunoni da dama sun ci albarkacin sallah inda suka samu ‘yanci daga dauri.
Fursunoni 90 daga cikin 3,898 an sake su ne a jiya daga gidan yarin Gorondutse a cikin bukukuwan sallar Idin Layya da ya gudana.
Gwamnan ya sanar da sakin fursunoni 90 din ne a lokacin da ya ziyarci gidan yarin cikin bikin sallah, inda Gandujen ya bada tabbacin cigaba da yin kyawawan ayyukan da suka dace har zuwa karewar wa’adin mulkinsa a 2023.
A cewarsa, “Wannan aikin na gudana ne bisa bin umarcin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman rage cinkoso a gidajen gyara halinmu.”
Gwamnan ya hori wadanda suka samu ‘yancin da su yi amfani da wannan damar wajen kyautata rayuwarsu na gaba tare da nemansu da su zama mutane na kwarai a cikin al’umma. Kazalika, ya tabbatar da cewa za su ci gaba da samar da abubuwan da suka dace a jihar.
An gano fursunonin na nuna matukar murnarsu da lale bisa afuwar da suka samu a karkashin Gwamnatin jihar.
Wadanda aka saken sun sha alwashin canza dabi’unsu na da tare da yin abuhuwa masu kyau a cikin rayuwarsu.
A jawabinsa, Kwanturolan gidan yarin Kano, Sulaiman M Inuwa ya jinjina wa gwamnan bisa wannan kyawawan aikin alkairin da ya yi, “a tsawon shekaru na 30 da na yi ina aiki, ban taba ganin gwamnan da ya yi irin wannan ba.”