Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano, M. A. Lawal, ya ce, babu wani abun da zai dakatar da gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga ciki alkawarin da ya dauka na rattaba hannu kan takardar kisa ga makashin karamar daliba ‘yar shekara biyar, Hanifa da zarar aka kammala cika ka’idojin da shari’a ta gindaya.
Kwamishinan wanda yake magana kan mataki na gaba da gwamnatin jihar zata dauka kan matsayar hukuncin da mai shari’a, Usman Na’aba, ya yanke, ya yi bayanin cewa mutum biyun da aka yanke wa hukuncin kisan su na da damar daukaka kara cikin wata uku zuwa kotun gaba da Kotun da ta yanke musu hukunci.
“Kotu ta yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya, don haka gwamna ya yi alkawarin sanya hannu kan hukuncin kisa, don haka muna jiran kwanaki 90 su cika na damar daukaka kara kafin aiwatar da hakan,” Cewar Kwamishina.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa alkawarin da suka yi tabbas a shirye suke su aiwatar amma dole su bi ka’idoji da matakan da shari’a ta ware wajen aiwatar da hakan.
Idan za ku iya tunawa dai Mai Shari’a Na’aba na babban kotun jihar Kano a makon jiya ya zartar da hukunci kan Tanko Abdulmalik, wanda ake zargi da kashe Hanifa, wanda kotun ta kama su dumu-dumu da laifin yin garkuwa da kashe karamar Dalian ‘yar shekara biyar a Kano wato Hanifa.
Inda kotun ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa har sai sun mutu.
Sannan kuma kotun ta yanke wa Abddulmalik da abokin aikata laifin nasa hukuncin shekara biyar a gidan kurkuku bisa sauran laifuka uku da ta samesu da aikatawa daga cikin tuhume-tuhumen da ake musu.
Kazalika, wacce ake zargi ta uku, Fatima Musa, kuma an yanke mata hukuncin shekara biyu a gidan gyara halinka bisa samunta da aikata babban laifi da kokarin yin garkuwa.
Antoni Janar din ya kara da cewa, “A cikin wata shida, Alkali ya kammala shari’ar. Wannan abun jinjina ne. Idan suka daukaka kara za mu sanar da jama’a cewa a shirye muke da hakan a kowani lokaci.
“Ga mutanen da suke ta jefa ayar tambaya kan ko shin za a aiwatar da hukuncin ko a’a, duk abun da zan ce shi ne doka dai doka ce kuma zamu jira kwanaki 90 din da suke da damar daukaka kara su yi.
Idan sun daukaka kara, shi kenan, nan da nan za mu dauki matakin hakan, idan kuma ba su daukaka kara ba har lokacin ya wuce gwamnati za ta aiwatar da abun da ya dace.”