Mambobin majalisar wakilai da suka kafa kungiya na ‘yan majalisa masu neman kawo sauyi a mabambantan jam’iyyun siyasa (G-30), suna neman a mayar da wa’adi daya na shuganba kasa da gwamnoni na tsawon shekara 6 tare da bayar da damar yin karba-karba na ofishin shugaban kasa ga dukkan shiyoyin kasar nan, a jerin kudrin da aka gabatar a zauren majalisar wakilai.
Haka kum ‘yan majalisar sun bayar da shawarar yadda za a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya da na gwamnoni da na majalisun jihohi da na kananan hukumomi ciki har da na Abuja a rana daya.
‘Yan majalisar masu nema kawo sauyi sun bayyana hakan ne a lokacin da suke ganawa da manema labarai kan wasu kudirori guda 50 da suka gabatar wadanda sun tsallake karatu na farko a majalisar wakilai a Abuja ranar Litinin.
- Ƙungiyar Likitocin Kano Za Ta Tsunduma Yajin Aiki
- Likitocin Kasar Sin Sun Taimakawa Al’ummun Saliyo Da Dabarun Yaki Da Malaria
Da yake karanta jawabin taron manema labarai, asalin wanda ya gabatar da kudirin kuma dan majalisar mai wakiltar mazabar Ideato ta Arewa/Kudanci ta Jihar Imo, Hon. Ikenga Imo Ugochinyere, ya ce suna ba da shawarar yin gyare-gyare ga kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999, wanda aka yi wa kwaskwarima, don samar da tsarin karba-karba na madafun iko a tsakanin shiyyoyi shida na siyasa na kasar nan wajen tabbatar da daidaiton wakilci tare da rage matsananciyar damuwa da tashin hankali na kirkirar sabbin jihohi.
Ugochinyere ya kuma bukaci a yi wa kundin tsarin mulki garambawul don samar da ofishin mataimakan shugaban kasa guda biyu daga yankin kudu da arewacin Nijeriya, inda mataimakin na daya ya zama cikakken mataimakin shugaban kasa, yayin da mataimakin na biyu ya kasance minista mai kula da tattalin arziki kuma dukkansu ministoci.
Ya ci gaba da cewa, kudirorin suna neman a yi wa kundin tsarin mulki gyara ne don ganin cewa shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa na daya za su fito ne daga yankuna duban-daban (Arewa ko Kudu), kuma mataimakin shugaban kasa na daya zai zama shugaban kasa a duk lokacin da shugaban kasa ya gaza.
“Mu zababbun ‘yan majalisar wakilai masu nemo wa al’ummar Nijeriya sauyi mun mayar da hankali ne wajen tabbatar da cewa muna da cikakkiyar damar ganin mun kula da al’amuranmu tare a matsayinmu na kasa guda. Don haka, a cikin kokarinmu na farko a cikin kudirinmu, mun gabatar da kudirori da shawarwari a zauren majalisa na 10. Wadannan kudirori za su tabo kowane fanni na ci gaba a dukkan bangarorin tattalin arzikinmu da kuma walwalarmu a matsayin kasa guda.
“Wadannan kudirorin da adadinsu ya kai 50 sun tsallake karatu na farko, amma a yau za mu fara gabatar wa mutane kusan 6 daga cikinsu, yayin da sauran za su zo nan da makonni masu zuwa. Guda 6 sun hada da sake fasalin harkokin mulki, tattalin arziki, tsaro, da adalci da sake fasalin dokokin zamantakewa da za su hada kan al’ummarmu da tabbatar da dorewar zaman lafiya da hadin kan kasa.
“Saboda haka, mun gabatar da kudirorin a yau wadanda za suka yi daidai da shawarwarin da muka bayar.
“A bangaren shugabanci kuwa, mun gabatar da shawarwari kamar haka:
“Sauya tsarin mulki don ba da damar yin karba-karba mulki a tsakanin shiyoyin siyasa guda shida don tabbatar da wakilci, daidai da rage bacin rai da yanayin tashin hankali don kirkirar jihohi.
“A yi wa sashe na 3 na kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin a amincewa da rarraba madafun iko ga dukkan shiyoyin Nijeriya. A gyara kundin tsarin mulkin kasar nan wajen amincewa da wa’adin mulki guda na shekaru shida ga shugaban kasa da gwamnonin. Haka zai rage kashe kudade da almubazzaranci lokaci tafiyar da gwamnati da samun nagarta wajen gudanar da sha’anin mulki da zaman lafiyar kasa ta hanyar samar wa shugaban kasa da gwamnoni wa’adi guda na shekaru shida.
“A gyara kundin tsarin mulkin kasa domin samar da mukaman mataimakin shugaban kasa guda biyu daga yankin kudu da arewacin Nijeriya, mataimakin shugaban kasa na daya zai gaje shi, mataimakin shugaban kasa na 2 zai kasance minista mai kula da tattalin arziki, kuma dukkansu ministoci.
“Cin gashin kai kananan hukumomi ta hanyar samar da wani asusun hadaka na kananan hukumomi mai zaman kansa wanda kananan hukumomi ke kulawa da shi tare da bayar da hukuncin dauri na tsawon lokaci a gidan yari kan duk wanda ya yi amfani da kudaden kananan hukumomin ba bisa ka’ida ba.
“Gyara sashe na 162(5) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekara 1999, idan gwamnatin jiha ta gaza mika wa kananan hukumomin kudadensu, irin wannan gwamnatin jiha ba za ta sami damar karbar kudede daga gwamnatin tarayya ba.
“Zabuka za su kasance ta hanya guda daya tilo ta dimokuradiyyarmu, ta hanyar dawo da turbar siyasarmu, don haka dole ne mu daidaita tsarin zabenmu. Mun bayar da wadannan shawarar da kudirori don magance cin hanci da rashawa a cikin harkokin zabenmu.
“Gyara bangaren dokar zabe don tabbatar da cewa ba za a bayyana wanda ya lashe zabe daga jami’an INEC har sai an bayyana sakamakon zabe da jerin sunayen wadanda aka tantance, sannan kuma a tabbatar da cewa sakamakon zaben da za a bayyana shi ne tare da jerin sunayen masu jefa kuri’a ta na’urar BBAS ko kuma kowace na’ura.
“A gyara dokar zabe ta yadda duk wani jami’in INEC da ya bayyana sakamakon karya zai fuskanci hukunci mai tsauri. Gyaran dokar zabe da ta tanadi cewa duk wasu kararrakin da suka shafi zaben dole ne su kasance a yanke hukunci daga kotun sauraron kararakin zabe, kotunan daukaka kara da sauransu, kafin a rantsar da wadanda suka yi nasarar lashe zabe.
“Wannan babban jan aiki ne da ke gabanmu, kuma ba za a iya samun nasara ba har sai mun hada kanmu wuri daya. Aikinmu bai wuce gabatar da kudiri a gaban majali
sa ba,” in ji shi.