Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi cewa ƙauyuka 43 daga jihohi 14 na iya fuskantar ruwan sama mai yawa da ambaliya daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Satumba, 2025.
Wannan gargaɗin ya fito ne daga Cibiyar da ke Gargaɗi kan Ambaliyar Ruwa da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli.
- Hakimin Da Aka Sace A Jihar Kogi Ya Shaki Iskar ‘Yanci
- ‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutane 3 Da Ake Zargi Da Damfara A Kano
Jihohin da abin zai shafa sun haɗa da Ebonyi, Cross River, Kano, Zamfara, Taraba, Abia, Yobe, Plateau, Borno, Imo, Neja, Sakkwato, Kaduna da Akwa Ibom.
Ambaliyar ruwa ta riga ta raba mutane da dama da muhallansu a Nijeriya, ta lalata gonaki da gidaje.
Masana sun ce sauyin yanayi da kuma rashin ingantattun magudanan ruwa ne ke ƙara tsananta matsalar.
A gefe guda kuma, gwamnatin China ta ba da tallafin dala miliyan ɗaya ($1m) domin taimaka wa waɗanda ambaliyar ta shafa a Arewacin Nijeriya.
Ministan Tsare-tsare da Tattalin Arziƙi, Abubakar Bagudu, ya ce za a yi amfani da kuɗin yadda ya dace, yayin da Jakadan China a Nijeriya, Yu Dunhai, ya nuna goyon baya da jajensa ga mutanen da abin ya shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp