Cacar-baki ta barke tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin sarrafa rogo zuwa garin kwaki da ake kira da Ugep ‘Garri’. Ugep ‘Garri’, ana sarrafa shi ne a garin Ugep da ke a karamar hukumar Yakur a jihar Koros Ribas.
Musayar yawun a tsakanin masu ruwa da tsakanin a fannin ta kaure ne biyo bayan furucin da shugaban kungiyar masu sarrafa Garin Kwaki reshen jihar (CGAN), Mista Augustine Okua ya yi na gargadin al’ummar da ke Kudancin Nijeriya, da na kasa baki daya ma cewa su guji shan Garin Kwakin da ake sarrafa wa a yankin na Ugep.
- Mutane 8 Sun Mutu, 2 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kogi
- Harin Jirgin Kaduna-Abuja: Hukumar Jiragen Kasa Ta Yi Asarar Miliyan 53 A Cikin Watanni 5
A wata hira da Augustine ya yi zargin cewa, garin shan zai iya shafar kiwon lafiyar jama’ar da suka sha shi, ganin cewa, wasu masu sarrafa rogo a yankin zuwa Garin Kwaki suna yi a cikin gaggawa ba tare sun bar rogon ya gama tsanewa ba don kawai su samu kudi da wuri.
Ya ce, Gari na dauke da sanadarin cyanide masu nauyin gaske wanda kuma zai iya shafar kiwon lafiyar wanda ya yi amfani da shi ko kuma ya jawo mutuwar wanda ya yi amfani da su, inda ya yi nuni da cewa, akalla ya fi da cewa a bar rogon ya kai kwana uku kafin a fara soya shi don mayar da shi gari.
Sai dai, wannan kalaman na Augustine, bai yi wa sauran masu ruwa da tsaki a fannin daga ke a jihar dadi ba, inda wasun su suka mayar masa da kakkausar martani.
Wasu daga cikinsu, sun ce, Augustine ya yi furucin ne saboda gonarsa ta noman Rogo karamace, inda a yanzu ya ke son zama mai sarrafa gari, hakan kuma ya sa yake son ya tsorata ‘ yan Nijeriya da sauran masu yin amfani da shi da ake sarrafa wa a garin na Ugep.
Cif Okoi Obono-Obla, tsohon mai bai wa shugaba Muhammadu Buhari shawara kuma basarake a garin na Ugep, shi ma ya soki furucin na Augustine, inda ya ce Augustine na kawai son bata wa garin suna ne da kuma son hana wa samun Garin karbuwa a gun jama’a.
Ya ce, kamata ya yi Augustine a matsayin san a shugaban kungiyar ya dinga kare ‘yancin masu sarrafa shi zuwa gari, amma ba kawai ya shiga kafafen yada labarai ya yin batacin kan Garin da ake sarrafa wa a garin ba.
Ya kara da cewa, kamata ya yi kafin ya yi furucin ya faga da jin ra’ayoyin ta alummar Ugep da kuma sauran masu sarrafa rogon.
“Kamata ya yi Augustine a matsayin san a shugaban kungiyar ya dinga kare ‘yancin masu sarrafa rogo zuwa zuwa gari, amma ba kawai ya shiga kafafen yada labarai ya yin batacin kan garin da ake sarrafa wa a garin ba”.
Ya yi nuni da cewa, garin da ake sarrafa wa a yankin shi ne ya fi kyau a daukacin fadin kasar nan.
Shi ma Yariman yankin Mkpani Oka Ibor ya sanar da cewa, furucin na Augustine son nuna gawawar alummar garin ne da kuma bata masu suna, musamman manyan masu sarrfara rogo zuwa gari a garin.
Sai dai, wani masani a fannin sarrafa rogo zuwa gari a yankin Mike Kit Oka ya sanar da cewa, rogo na dauke da sanadarin cyanide kadan ne, sabanin sanadarin na cyanide da ke jikin sauran amfanin gona.