Tawagar kwallon kafa ta maza ta babban birnin tarayya Abuja FCT ta fara da kafar dama bayan ta lallasa tawagar jihar Borno da ci 4-1 a wasan farko da ta buga a ci gaba da gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta kasa (NSF) na shekarar 2024.
Tawagar ta FCT sun doke abokan karawarsu Borno da ci 4-1 a wasan da suka buga da safiyar Litinin a filin atisayen Remo Stars da ke Ikenne a jihar Ogun, dan wasan gaba Paul Joseph shi ne ya zura kwallaye har uku rigis a wasan, da take jawabi bayan nasarar, mataimakiyar kocin FCT kuma tsohuwar tauraruwar Super Falcons, Coach Mary Godspower Benny ta shaida wa manema labarai cewa sakamakon ya sanya kungiyar ta sake samun karsashi yayinda ta ke tunkarar wasa na gaba.
- Kasar Sin Ta Samu Bunkasar Masana’antar Harkokin Tauraron Dan Adam A Shekarar 2024
- Akwai Kure A Maganar Gwamna Kan Kulawa Da Masu Rauni – Ƙungiyar Dattawan Zamfara
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Tawagar Borno ta zura kwallo amma kuma hakan bai hana aka doketa da ci 4-1 a wasan ba, wasan gaba da Borno za ta buga zatayi fatan samun nasara domin samun damar cigaba da fafatawa a cigaba da wasannin da akeyi a birnin Abeokuta na jahar Ogun.
Kyaftin din kungiyar, Achu Gabriel, ya yabawa takwarorinsa da suka nuna kwazo, inda ya kara da cewa tawagar za ta ci gaba da mai da hankali wajen kwato kofin da ta lashe a shekarar 2018, tawagar ta Abuja za ta kara da mai masaukin baki, jihar Ogun a wasan rukuni na biyu a ranar Talata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp