ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gaskiya Ba Ta Buya…

by CMG Hausa
3 years ago

Idan ba a manta ba, a shekarar 2021 da ta gabata ne, Amurka ta kira taron demokiradiya, amma tun kafin lokacin wasu masharhanta ke ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi game da wannan taro da ma ma’anarsa.

Bisa kalamai da jami’an Amurka suka sha furtawa, wai manufar taron ita ce wai yin bita, game da nasarorin da Amurka da kawayenta suka cimma a fannin karewa, da aiwatar da salon mulkin dimokaradiyya.

  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Kasar Amurka A Indonesia

To amma abun tambaya a nan shi ne, wace nasara tsarin demokiradiyar yamma ya haifar ga ita kanta Amurka da ma duniya?
Amsar wannan tambaya a bayyane take.

ADVERTISEMENT

Idan muka yi la’akari da yanayin da duniyarmu take ciki a yanzu na fuskantar kalubaloli masu tarin yawa, kama daga koma bayan tattalin arziki, zuwa yaduwar cutar numfashin ta COVID-19, da yadda wannan annoba ta karade kasashen duniya manya da kanana, ciki har da Amurka ita kanta, inda ta yi mummunar barna. A fili take cewa, Amurka ta gaza wajen shawo kan wannan matsala, da ma sauran kalubalolin dake addabar kasar a cikin gida. Don haka, tsarin ya gaza a dukkan fannoni.

Na baya-bayan shi ne, wani sakamakon bincike da kafar yada labaran BBC ta wallafa dake nuna cewa, Larabawa ma sun yanke kauna kan tsarin demokuradiyyar yammacin duniya, a kokarin samar da daidaiton tattalin arziki a yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka.

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Rahoton ya ce, sama da rabin mutane 23,000 da cibiyar sadarwa ta Arab Barometer ta zanta da su a fadin yankin, sun amince cewa, tattalin arziki ya yi rauni a karkashin tsarin demokuradiyya na kasashen yamma.

Ana kara fahimtar cewa, tsarin demokuradiyyar yammacin duniya, ba cikakken tsarin gwamnati ba ne, kuma ba zai iya taba gyara komai ba.

Abin da wadanda suka gudanar da bincike suka gani da idonsu a fadin yankin shi ne, mutane na fama da yunwa, mutane na bukatar buredi, mutane na nuna takaici da tsarin da suke amfani da shi.” Galibin wadanda aka zanta da su, ba sa tsammanin yanayin tattalin arzikin kasashensu zai inganta a cikin ’yan shekaru masu zuwa.

Haka kuma, an ga yadda Amurka ke dandana kudar tsadar rayuwa, baya ga yadda sassan ’yan kasar ke kokawa game da rasa damar fadin albarkacin baki, da uwa uba matsalar kare hakkin bil adama, ta yadda kawo yanzu sanadiyyar bazuwar cutar COVID-19 kadai, dubban daruruwan Amurkawa suka rasa rayukan su.

Masu fashin baki na cewa, duk tsarin jagorancin da ya gaza wajen sauke nauyin kare rayukan al’umma, suka kuma kasa daidaita matsalolin tattalin arziki, da na zamantakewar al’ummarsu yadda ya kamata, shin anya kuwa ya dace su rika ambaton ko da sunan tsarin ma?
A takaice dai, bai dace kasashen duniya dake da ’yanci su rika barin masu ragin tsarin demokiradiyar yamma su rika amfani da su, da sunan kare demokaradiyya, a rika haifar da rarrabuwar kawuna ba.

A maimakon haka, kamata ya yi a mayar da hankali ga hadin gwiwar dukkanin sassan, wajen warware kalubalolin bai daya dake addabar daukacin bil adama, kuma lokaci zai kara fayyace boyayyun manufofin Amurka game da batun tsarin demokiradiya har da kokarin kare shi.

Tsarin demokuradiyya na kasar Amurka, wani sakamako ne da kasar ta samu bisa gwajin da ta yi ita kadai a cikin gidanta, don haka ba dole ne ya dace da sauran kasashe ba.

Saboda haka, kasar Amurka ba ta da ikon yin babakere game da mizanin demokuradiyya, da fakewa da maganar demokuradiyya wajen neman kulla kawance tare da wasu kasashe, da neman ta da rikici a duniya. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara
Daga Birnin Sin

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Mai Gadin Kabarin Manzon Allah SAW Ya Rasu

Mai Gadin Kabarin Manzon Allah SAW Ya Rasu

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.