NAFDAC ta karyata maganar jita jitar da ake yi mai nuna cewa allurar rigakafin da ake yi ma kananan yara,a Nijeriya ta kunshi kashi 40 na sinadarin mercury,wanda kamfanin kasashen waje ya amince da bada umarnin ayi amfani da shi.
Babbar jami’a kuma Shugabar hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye, ita ta bayyana hakan a wani jawabin da aka rabawa manema labarai, ta kuma ce mercury zaiba ce don haka ba za a iya amfani da ita ba a matsayin wani sinadari wajen yin allura.
- Kammala aikin tashar ruwa mai zurfi ta Lagos zai ingiza bunkasar tattalin arzikin Najeriya
- CHEC Ya Mika Tashar Teku Mai Zurfi Ta Farko Ta Najeriya
Abubuwan da ake amfani da su wajen sinadaran yin alluran rigakafi irinsu antigens, adjubants domin su taimaka wajen bunkasa yadda allurar zata yi maganin daya kamata ta yi.Kamar dai yadda antibiotics suke hana gurbacewar maganin lokacin da ake yin shi, da kuma adanawa da daidaitawa. Bugu da kari kuma yana murkushe kwayoyin cuta wadanda idan ba, suna iya yi ma jiki illar gaske ta hanyar zama sanadiyar kamuwa da cuta.
Adeyeye ta bayyana cewa shi sinadarin thimerosal wani nau’i ne na mercuric daya kunshi abubuwa fiye da biyu,ana amfani da shi ne na,nau’i nau’i na allurai,ya kunshi wani nau’i na mercury mai suna ethyl mercury.
“A matsayin abinda ake kiyayewa da shi wajen adana allura ana amafani da, thimerosa wajen adana kashi 0.003 ya koma zuwa kashi 0.01,( alal misali,sinadarin thimerosal da aka amince da shi a allurai shi ne tsakanin sassa 30 zuwa mafi yawa da ya kai of 100 daga cikin sassa milyan daya na abinda ya dace na allurar ta kunsa)Thimerosal wani sinadari ne da ake amfani da shi wajen adana abu a kasar Amurka wanda aka yi amfani da shi shekaru masu yawa da suka wuce.
Ta kara jaddada cewa babu wata sheda dake nuna ana samun matsala idan har sinadarin thimerosa ya kasance dan kadan a cikin allura sai dai kuma ana iya samun matsala ta yadda wurin da aka yi allurar yake yin ja,ko kuma ya kumbura.
Kamar yadda ta yi karin bayani “A watan Yuli na shekarar 1999, hukumomin kula da lafiyar al’umma na cibiyar kula da cututtukan yara ta kasar Amurka.
Su da masu yin alluran rigakafin na cututtukan yara sun amince shi sinadarin thimerosal ana iya rage shi a cikin alluran,ko kuma gaba daya kada a sa shi,a matsayin wani mataki na kada a bari abin da zai hana samar da matsalar da zata kai ga cutarwa.Kamar dai yadda bayanin nata ya nuna”.
Ta cigaba da bayani mai nuna duk da yake dai kasar Nijeriya tana samun alluran da suka kunshi sinadarin thimerosal amma kuma a matsayin iyakar mizanin da aka amince da shi na sinadarin.Shugabar ta NAFDAC tace hukumar lafiya ta duniya (WHO) tana cigaba da sa ido akan shedar ilmin kimiyya da take nasaba da amfani da thimerosal a matsayin allura fiye da shekara goma, bama kamar ta hanyar mai bada shawara mai zaman kansa, kwamitin bada shawara kan al’amarin da ya shafi alluran rigakafi na duniya.
“Lokaci zuwa lokaci kwamitin ya kan cimma matsaya mai nuna cewa ba wata sheda da take nuna irin mizanin sinadarin thimerosal da ake amafani da shi a alluran rigakafi,zai iya kasancewa wata matsalar da zata shafi lafiya
Sauran kungiyoyin kwararrun sun hada da cibiyar magunguna ta kasar Amurka, hadaddiyar cibiyar ilmantarwa ta al’arin daya shafi cututtukan kananan yara ta Amurka. Cibiyar da ke kulawa da ingancin magunguna na nahiyar Turai, sai kuma hukuma mai kula da duba yadda kayayyakin magunguna ya dace su kasance, duk sun cimma matsaya.
Daga karshe ta ce hukumar NAFDAC za ta cigaba da bin sharuddan da hukumar lafiya ta duniya ta amince dasu, kafin a kai ga yin amfani da duk wata allura a Nijeriya.