Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage ƙarar tsohon gwamnan Kogi Alhaji Yahaya Bello zuwa ranar 27 ga watan Yuni. Mai shari’a Emeka Nwite ya sanya sabuwar ranar ne bayan lauyan da ke ƙara Adeola Adedipe ya shaida wa kotun cewa babban Lauyan EFCC, Kemi Pinhero, ya buƙaci a sauya musu wata ranar don ci gaba da shari’ar.
Adedipe, ya yi mamakin kasancewar lauyan EFCC, Oyedepo, ya bayyana cewa akwai yarjejeniyar tura ƙananan lauyoyin da za su sake nemo sabuwar sauraron ƙarar. Ya kuma jaddada shirye-shiryen tsohon gwamnan, inda ya bayyana cewa babu bukatar zuwansa idan har za a saka sabon ranar.
- Kotu Ta Hana EFCC Kama Rabi’u Musa Kwankwaso
- Daga Karshe EFCC ZA Ta Gurfanar Da Yahaya Bello A Kotu
Oyedepo ya musanta sanin irin wannan yarjejeniya, lamarin da ya sa babban lauya Simon Lough ya shiga tsakani, wanda ya ba da shawarar sanya wata sabuwar rana ba tare da wata hujja ba.
Mai shari’a Nwite ya amince kuma ya ɗage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Yuni, inda ya tabbatar da dole ne wanda ake ƙara ya bayyana a shari’a mai zuwa.