Hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta bayyana a jiya Laraba cewa, yawan kudin da kasar ta samu daga kayayyaki da hidimomi da ta samar ko GDP a takaice, ya karu da kashi 5.2 cikin dari a cikin farkon watanni 9 na shekarar 2023 idan aka kwatanta da makamancin lokaci na bara.
Kididdigar ta NBS ta nuna cewa, GDPn kasar Sin ya kai fiye da yuan tiriliyan 91.3 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 12.7 a cikin farkon watanni 9 na shekarar.
A rubu’in na uku, GDPn kasar ya karu da kashi 4.9 cikin dari idan aka kwatanta da makamacin lokaci na bara, kamar yadda NBS ta bayyana. (Muhammed Yahaya)
Talla