Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Kashim Shettima, wanda ya halarci taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa, kan shawarar ziri daya da hanya daya wato BRF karo na uku a nan birnin Beijing.
Yayin zantawar ta su, shugaba Xi ya ce hadin gwiwar Sin da Najeriya a fannin gina shawarar ziri daya da hanya daya na cikin kyakkyawan yanayin bunkasuwa, kuma daya ne daga ginshikan hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka.
- Kasashe Masu Tasowa Da Abokai Sun Goyi Bayan Matsayin Kasar Sin Mai Adalci A Taron MDD
- Xi Ya Sanar Da Matakai 8 Na Tallafawa Raya Hadin Gwiwar Shawarar BRI Mai Inganci
Ya ce hadin kai, da hadin gwiwa tsakanin Sin da Najeriya, a matsayin su na kasashe biyu dake kan gaba a jerin kasashe masu tasowa, ya dace da tafarkin da ake kai yanzu, na bunkasar kasashe masu tasowa, da masu saurin bunkasar tattalin arziki, kuma hakan ya yi daidai da bukatun kasashen biyu.
Har ila yau a Larabar nan, shugaba Xi ya gana da shugaban kasar Kenya William Ruto, da na Argentina Alberto Fernandez, da kuma babban magatakardar MDD Antonio Guterres. (Mai fassara: Saminu Alhassan)