Daya daga cikin masu shirya fina-finai a masana’antar Kannywood, Darakta kuma jarumi a masana’antar; Falau A. Dorayi ya yi karin haske dangane da yadda ya kamata masana’antar ta mayar da hankalin, duba da cewa; yanzu kida ya canza, don haka; rawa ma ta canza.
A cewar Dorayi, an matukar samun sauyi a wannan masana’anta, ta fuskar samun kudade; ba kamar da ba. A wata hira da ya yi da RFI Hausa, Falalu ya bayyana cewa; ya fara fim tsawon shekaru da dama da suka shude, inda ya bayyana cewa; duba da yawaitar gidajen Gala a fadin Nijeriya, ya sa yake ganin wannan ita kadai hanya mafi bullewa.
- INEC Ta Ayyana 16 Ga Agusta Don Gudanar Da Zaben Cike Gurbi A Jihohi 12
- Sin Da Ghana Za Su Karfafa Hadin Gwiwarsu
“Duk da cewa, har yanzu masana’antar ta Kannywood babu laifi; ana samun kudade, amma dai akwai bukatar a fadada hanyoyin samun kudaden shiga a masana’antar, wanda kuma a halin yanzu babu wata hanya da ta fi nuna fina-finai a gidajen Galar, yanzu haka; idan ba don samun tashar ‘Youtube’ da aka yi ba, da ba a nsan yadda masana’antar za ta kasance ba”, in ji shi.
Ya kara da cewa, misali akwai daruruwan masu sana’ar ‘downloading’ a Arewacin Nijeriya, amma kwata-kwata abin da suke biya bai fi Naira miliyan daya zuwa biyu ba, sannan kuma ba kowa ne ke iya saka data ya kalli fim a shafukan yanar gizo ba, kowa ya fi son idan abokinsa ko kawarta ta dauko; sai ya tura masa ko ta tura mata ba tare da sun kashe ko sisi ba, kazalika kuma a ‘YouTube’ ne kadai wanda ya dauki nauyin fim zai iya dan samun wani abu mai dama-dama, idan an kalla.
“Tun lokacin da aka daina buga faifan CD a masana’antar Kannywood, samun kudade ya ja baya, amma yanzu ake neman hanyoyin da za a bi, domin warware wadannan matsaloli, don haka a ganina; kamata ya yi a dawo inda aka bari, tunda har aka gano cewa; masu sha’awar kallon fina-finan Hausa, za su iya zuwa gidajen Gala tun daga karfe biyar na yamma zuwa lokacin sallar Magriba, sannan kuma su sake dawowa daga karfe 8 zuwa 12 na dare, su biya kudi don kallon fina-finan da ake haskawa a wadannan wurare, me zai hana mu mayar da akalarmu zuwa wajensu?” in ji shi.
“Ni na san fina-finan da aka haska a gidajen Gala da aka samu fiye da Naira miliyan daya a rana daya, wasu kuma har miliyan biyu, yanzu idan ka duba tun daga Kano har Nijar za ka dinga ganin gidajen Gala, haka zalika daga nan Kano har zuwa birnin Legas ma akwai su, saboda haka; me zai hana mu rika amfani da wannan dama wajen fadada adadin kudaden shiga da wannan masana’anta mai albarka take samu?
Daga karshe, ya bukaci hadin kai daga dukkanin wasu masu ruwa da tsaki, wajen ganin wannan haka ya cimma ruwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp