Wasu mazauna Jihar Kano sun bayyana damuwarsu kan karin kudin shiga gidan wanka da ba-haya, wanda ya kai kusan kashi 70 cikin 100 a baya-bayan nan.
BBC Hausa ta ruwaito cewa lamarin na zuwa ne, daidai lokacin da ake kokawa kan hauhawar farashin kaya da na ayyuka, sakamakon cire tallafin man fetur da kuma faduwar darajar naira a kasuwar canji.
Mutane kan shiga gidajen wanka ne don yin ba-haya ko wanka da wanki da kama-ruwa ko fitsari, kai har ma da alwala.
Sai dai, masu gidajen wanka a Kano yanzu duk sun kara kudadensu, yayin da tashin farashin yin ba-haya da kama ruwa, ya fi tayar da hankula, saboda kasancewarsa bukatar da ta zama dole.
Yanzu haka dai mazauna jihar sun shiga damuwa kan karin da gidajen wankan suka yi.
Leadership Hausa ta bibiyi wasu daga cikin gidajen wankan, inda suka ce tashin kayayyaki ne ya haifar da nasu karin.
Sai dai wasu na ganin akwai bukatar mahukunta su shiga lamarin don daidaita al’amura.