Gidauniyar TY Burutai ta mika sakon taya murna ga Kwamanda Tunde Giwa Daramola kan zama shugaban kungiyar masu tseren kwale kwale ta Jihar Ondo.
Wanda Gwamnan jihar wato Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya nada shi. Sakon taya murnar ta fito ne ta hannun Shugaban Gidauniyar, Ibrahim Dahiru Danfulani Sadaukin Gwarkuwan Keffi/Betara Biu wanda ya mika wa manema labarai.
- MOFA: Ministan Harkokin Wajen Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin
- Xi Ya Amsa Wasikar Wakilan Daliban Da Suka Halarci Gasar Kere-Keren Kimiyya Ta Kasa Da Kasa Ta Kasar Sin
Kwamanda Tunde Giwa Daramola mai ritaya mutum ne da ya yi fice daga cikin tsarraraki kuma babban abin alfahrin dalban makarantar sojoji da ke Kaduna aji na 29. Ba kawai babban soja ba ne ya kuma kasance kwararren ma’aikaci. Yanayin tafiyar da al’amuran shi da kuma maida hankali wajen aiki da kuma wasannin motsa jiki ya zamar dashi wanda ya cancanci wannan mukami.
Uban Gidauniyar TY Burutai, wato Ambasada Janar Tukur Yusuf Buratai tsowan shugaban sojojin Nijeriya ya yi matukar murna da jin dadi game da wannan nadin da a ka yi ma Kwamanda Giwa Daramola.
Ya Kuma jadadda muhimmancin samun shugaba kamar Giwa Daramola a shugabancin wannan kungiya. A cewar sa; “Kwamanda Giwa Daramola yana da ruhin dagiya da kwarewa a harkar motsa jiki wanda matasan mu suke bukata a matsayin abin koyi” Ya kara da cewa “Kwarewar shi da kuma maida hankalin shi ga ci gaba ba bu shakka zai daga Kungiyar zuwa matakin da ya kamata”
Gidauniyar tana alfahari da tallafa wa shugabanni kaman Kwamanda Giwa Daramola wanda suka tsayu da gaskiya da rikon amana a wajen aiki. Muna da yakini karkashin jagorancinshi na Shugaban kungiyar Masu Tseren Kwale kwale Na Jihar Ondo zai samar da ci gaba da sabbin masu wasannin motsa jiki a fadin jihar.
Muna jinjina wa gwamnatin jihar Ondo a kan wannan nadi inda gwamnan yayi duba da kwarewa a harkar tsaro da kuma kokari a fannin motsa jiki wajen wannan nadin. Gidauniyar TY Buratai ta shirya tsaf domin ganin irin ci gaban da za a samu karkashin shugabancin Kwamanda Giwa Daramola a jihar baki daya.
A halin yanzu yabo da jinjina sai kara fitowa yake yi ga shugaban kasa Tinubu a kan yadda ya dauki sashen samar da wutar lantarki a Nijeriya da matukar muhimmanci. Yabo na baya-bayan nan ya fito daga wata kallabi a tsakanin rawunna, Injiniya Amina Ahmed a yayin babban taron makashi na kasa da aka yi a garin Legas a makon jiya.
Taron ya tara masana daga sasan kasar inda aka tatauna yadda za a bunkaasa hanyoyin samar da makashi ga al’ummar Nijeriya gaba daya
Ta bayyana cewa, samar da cikakken wutar lantarki zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin al’umma. Ta ce, bunkasa hanyoyin samar da lantarki ta hanyar hasken rana, zai taimaka wajen bunkasa sana’o’in al’ummar karkara.
Daga nan kuma Injiniya Amina Ahmed ta yi kira gan mata musamman na karkara da su nemi Ilimi tare da rike sana’a, “Ba sai sun nemi sana’a ko aikin gwamnati ba, domin a wannan zamanin, gwamnmati ba za ta iya samar wa da al’umma aiki gaba daya ba, a kan haka ta nemi sauran al’umma musamman masu hannu da shuni da su rika tallafa wa matasan da ke unguwanni ko garuruwansu da shawarwari da kuma tallafi don su samu dogaro da kawunansu.
Daga karshe ta yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kan yadda ya dauki lamarin samar da wutar lantarki da matukar muhimanci. Za a iya lura da haka ne ta hanyar da ya zabi wadanda suke jagorantar ma’aikatar wutar lantarki musamman Minista Hon Adebayo Adelabu, ‘Hon Adebayo Adelabu ya jajirce wajen tattabar da an tsaftace harkar bayar da wutar lantarki a Nijeriya, in ji ta.