Akalla mutum 12,300 masu dauke da cutar kaba gidauniyar Alhaji Dahiru Mangal ta yi wa aiki kyauta a Jihar Katsina.
Kamar yadda daya daga cikin ‘yan kwamitin amintattu na gidauniyar, Malam Hussaini Kabir ya shaida wa manema labarai a Katsina a lokacin kaddamar da aikin tiyatar kashi na biyu.
- Gwamnan Zamfara Ya Kai Wa Mangal Ziyarar Ta’aziyya
- Mangal Ya Dauki Nauyin Yi Wa Masu Ciwon Mafitsara 80 Aiki A KatsinaÂ
Ya bayyana cewa gidauniyar tana gudanar da wannan aiki ne kyauta ga marasa karfi duk bayan wata uku tun daga lokacin da aka kafa gidauniyar a shekarar 2013.
Ya kara da cewa mutum 500 zuwa 600 ne suke amfana da wannan aiki na cutar kaba duk bayan watanni uku da ake gudanar da aikin.
“Wadannan ayyuka da muke yi ba wai sun tsaya ba ne kan mutanen Katsina ba, har da makwabtan jihohi suna amfana da wannan gudummawan” in ji Malam Hussaini.
A cewarsa, baban dalilin da ya sa suke wannan aiki shi ne, domin a rage wa al’umma musamman masu karamin karfi wahalwalun da suke sha wajen neman lafiya.
Malam Hussaini ya yi kira ga sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni da su ba da tasu gudummawa wajen irin wannan aiki ta yadda za su taimaka wa kokarin gwamanti kan harkokin kiwon lafiya.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da wannan taimako na aikin kaba sun yaba da kokarin wannan gidauniya, inda suka ce hakan zai taimaka wa kokarin gwamanti da sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni da su yi ko yi da wannan gidauniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp